Connect with us

News

Rikici Ya Tilasta Mutane Sama Da Dubu 6,000 Ƙetara Wa Nijar Daga Najeriya A Cikin Shekara Guda

Published

on

IMG 20261111 105702 279
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kusan mutane dubu 64,000 ne suka ƙetara Nijar daga arewacin Najeriya cikin wannan shekara ta 2026, saboda rikice-rikice.

Hukumar UNHCR ta Majalisar Ɗinkin Duniyar ta ce dubban ƴan Najeriya sun ƙetare Nijar ne don kauracewa hare-haren ƴan ta’adda da masu tada ƙayar baya da suka addabi arewacin ƙasar.

Rikici Ya Tilasta Mutane Sama Da Dubu 6,000 Ƙetara Wa Nijar Daga Najeriya A Cikin Shekara Guda

Lamarin ya ƙara ta’azzarar matsalar agaji da ake fuskanta a Nijar da yanzu haka take zama mafaka ga ƴan ci rani fiye da dubu 500,000, ciki har da na Najeriya dubu 327,500.

Rahoton ya ce wasu ƙarin ƴan Najeriya na daban kuma sun tsere zuwa jamhuriyar Benin don samun mafaka.

Mafi yawan waɗanda suka tsallaka Nijar ɗin na zama a yankunan dake kusa da iyakar Najeriya da maƙwabciyarta ta, wato Diffa da Tahoua, kuma fiye da mutane dubu 23,000 kashi 2 bisa 3 na adadinsu ƙananan yara ne waɗanda suka isa Diffa kaɗai tun daga farkon shekarar nan.

Advertisement

A halin yanzu, hukumar dake kula da ƴan gudun hijirar na neman tallafin dala miliyan 11 da dubu 400 don faɗaɗa ayyukan agaji a ƙasashen Nijar, da Najeriya da Benin, tana mai gargaɗin yiwuwar gaza tallafa wa dubban mutanen da rikicin ya raba da muhallansu.

 

 

RFI HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending