News
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wata Mace Mai Shekaru 54 Kan Zargin Garkuwa Da Kanta

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta cafke wata mata mai shekaru 54, mai suna Umadi, bisa zargin shirya garkuwa da kanta domin karɓar kuɗin fansa naira miliyan 15 daga hannun ƙaninta.
Matar ta yi ikirarin cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ita lokacin da ta fita sayen magani, inda ta yi barazanar cewa za a kashe ta idan ƙaninta bai biya kuɗin fansar ba.
ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Jami’ar Zamfara
Sai dai binciken ’yan sanda ya gano cewa ita da kanta ta shirya lamarin domin karɓar kuɗin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Bright Edafe, ya ce an kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda na Ogwashi-Uku a ranar 23 ga Oktoba, 2026.
Ya bayyana cewa matar ta amsa laifin shirya garkuwa da kanta, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutanen da ake zargin sun taimaka mata wajen aikata laifin.
