News
ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Jami’ar Zamfara

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Zamfara, ta tsunduma yajin aiki marar ƙayyadadden lokaci sakamakon rashin biyan buƙatunta da suka shafi walwalar ma’aikata, albashi, ƙarin girma da inganta yanayin aiki.
Shugaban reshen ƙungiyar, Comrade Anas Abubakar Dogo, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce matakin ya biyo bayan gazawar mahukuntan jami’ar wajen magance matsalolin da ƙungiyar ta shafe tsawon lokaci tana gabatarwa.
An Kashe Mutane 418, An Yi Garkuwa Da 227 Cikin Watanni Biyu A Nijeriya — Rundunar Ƴansanda
Ya bayyana cewa ƙungiyar ta fara da bai wa mahukuntan jami’ar wa’adin makonni biyu domin su magance matsalolin, daga bisani kuma ta ƙara da wasu makonni uku, amma har yanzu ba a samu biyan buƙatunta ba.
A cewarsa, ƙungiyar ta kuma gudanar da yajin aikin gargaɗi na tsawon mako guda domin matsa wa mahukuntan jami’ar lamba, amma rashin samun mafita ya sa ta ɗauki matakin shiga yajin aiki marar ƙayyadadden lokaci.
Dogo ya ce daga cikin matsalolin da suka tilasta ɗaukar matakin akwai rashin ɗakunan kwanan ɗalibai na jami’a, ƙarancin gidajen zama ga ma’aikata, ƙarancin albashi da rashin aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta ƙulla da ASUU.
Ya bayyana cewa ɗaliban jami’ar ba su da masaukin hukuma, yayin da malamai da sauran ma’aikata ke fuskantar ƙarancin gidajen zama, lamarin da ya ce yana kawo cikas ga gudanarwa da bunƙasar jami’ar.
Haka kuma, ya zargi mahukuntan jami’ar da kasa aiwatar da dukkan tanade-tanaden yarjejeniyar gwamnatin tarayya da ASUU, ciki har da biyan basussukan da ake bin malaman jami’ar.
Shugaban ƙungiyar ya kuma nuna damuwa kan rashin aiwatar da ƙarin girman ma’aikata da kuma biyan kuɗaɗen haƙƙoƙin ƙarin girman da suka taru, yana mai cewa hakan na rage ƙwarin gwiwar malamai.
Dangane da ƙarancin ma’aikatan koyarwa kuwa, Dogo ya bayyana cewa wasu sassan jami’ar na da malami guda ɗaya kacal mai cikakken matsayin aiki, yayin da wasu sassan ba su da ko malami guda ɗaya.
Ya yi gargaɗin cewa wannan yanayi na iya shafar ingancin koyarwa, bincike da sauran harkokin ilimi a jami’ar.
Ya kuma bayyana Jami’ar Jihar Zamfara a matsayin wurin horas da malamai da daga bisani suke barinta zuwa wasu jami’o’i saboda neman ingantaccen albashi da yanayin aiki.
A ewarsa, wasu daga cikin malaman jami’ar na karɓar albashin wata-wata tsakanin naira 96,000 da naira 120,000, adadin da ya ce bai wadatar da bukatunsu ba, kuma yana cikin dalilan da ke sa jami’ar fuskantar matsalar riƙe ƙwararrun malamai.
ASUU ta buƙaci mahukuntan jami’ar da su aiwatar da dukkan tanade-tanaden yarjejeniyar gwamnatin tarayya da ƙungiyar, su biya dukkan basussukan da ake bin malamai, tare da aiwatar da ƙarin girma da biyan haƙƙoƙinsa.
Dogo ya bayyana cewa za a dakatar da dukkan ayyukan koyarwa da karatu a harabar jami’ar a tsawon lokacin yajin aikin.
Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta magance matsalolin domin kawo ƙarshen takaddamar da kuma ba da damar ci gaba da harkokin ilimi a jami’ar.
