Connect with us

News

ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki A Jami’ar Zamfara

Published

on

ASUU logo 1000x600 1 768x461 (1)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Zamfara, ta yi barazanar tsunduma yajin aiki marar ƙayyadadden lokaci daga ranar 13 ga Nuwamba, 2026, sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar mahukuntan jami’ar wajen biyan buƙatunta da suka shafi walwalar ma’aikata da inganta yanayin aiki.

Shugaban reshen ƙungiyar, Comrade Anas Abubakar Dogo, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce yajin aikin zai fara da tsakar daren ranar 13 ga Nuwamba.

An Kashe Mutane 418, An Yi Garkuwa Da 227 Cikin Watanni Biyu A Nijeriya  — Rundunar  Ƴansanda 

Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan ƙarewar wa’adin makonni biyu da ƙungiyar ta bai wa mahukuntan jami’ar, wanda daga bisani aka ƙara da wasu makonni uku, amma duk da haka ba a samu biyan buƙatun ƙungiyar ba.

A cewarsa, ASUU ta kuma gudanar da yajin aikin gargaɗi na tsawon mako guda domin matsa wa mahukuntan jami’ar lamba su magance matsalolin, amma rashin samun mafita ya tilasta mata ɗaukar matakin shirin shiga yajin aiki marar ƙayyadadden lokaci.

Dogo ya bayyana cewa daga cikin matsalolin da ƙungiyar ke fuskanta akwai rashin masaukin ɗalibai na jami’a, ƙarancin gidajen zama ga ma’aikata, ƙarancin albashi, rashin biyan basussukan malamai da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta ƙulla da ASUU.

Advertisement

Shugaban ƙungiyar ya kuma koka kan rashin aiwatar da ƙarin girman ma’aikata da kuma biyan kuɗaɗen haƙƙoƙin ƙarin girman da suka taru, yana mai cewa hakan na rage ƙwarin gwiwar malamai wajen gudanar da aikinsu.

Ya yi gargaɗin cewa wannan matsala na iya yin mummunan tasiri ga ingancin koyarwa, bincike da sauran harkokin ilimi a jami’ar.

Ya kuma bayyana Jami’ar Jihar Zamfara a matsayin cibiyar horas da malamai da daga bisani suke barinta zuwa wasu jami’o’i saboda neman ingantaccen albashi da yanayin aiki.

A cewarsa, wasu daga cikin malaman jami’ar na karɓar albashin wata-wata tsakanin naira 96,000 da naira 120,000, adadin da ya ce bai wadatar ba, kuma yana daga cikin dalilan da ke sa jami’ar fuskantar matsalar riƙe ƙwararrun malamai.

ASUU ta buƙaci cikakken aiwatar da dukkan tanade-tanaden yarjejeniyar gwamnatin tarayya da ƙungiyar, biyan dukkan basussukan da ake bin malamai, da kuma aiwatar da ƙarin girman ma’aikata tare da biyan haƙƙoƙin da suka taru.

Dogo ya tabbatar da cewa za a dakatar da dukkan ayyukan koyarwa da karatu a jami’ar a duk tsawon lokacin yajin aikin.

Advertisement

Ya yi kira ga mahukuntan jami’ar da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta magance matsalolin domin kauce wa katsewar harkokin ilimi da kuma tabbatar da ci gaba da karatu a jami’ar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending