News
Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Mataimakin Gwamnan Kano Kan Dakatar Da Shirin Tsige Shi
Wata Babbar Kotun Tarayya ta ki amincewa da bukatar neman umarnin wucin gadi da mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya gabatar domin dakatar da shirin tsige shi da majalisar dokokin jihar Kano ta fara.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito a hukuncin da mai shari’a S.M. Shaibu ya yanke a ranar 25 ga Maris, 2026, kotun ta bayyana cewa mai neman umarnin bai cika sharudan da ake bukata ba domin a ba shi wannan kariya ta gaggawa.
Haka kuma kotun ta umurce shi da ya mika takardun shari’ar ga wadanda ake kara domin su samu damar mayar da martani yadda ya kamata.
Tun da farko dai, majalisar dokokin jihar Kano ta samu wani umarni na wucin gadi daga kotu a ranar 11 ga Maris, 2026, wanda ya hana mataimakin gwamnan daukar duk wani mataki da zai kawo cikas ga aikin majalisar, musamman dangane da ikon da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ta karkashin sashe na 188.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
