Connect with us

Politics

Rashin Bayyanar Mataimakin Gwamnan Kano A Taron Majalisar Zartarwa Ya Jawo Cece-Ku-Ce Kan Matsayinsa

Published

on

images (9)

Mataimakin gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, bai halarci taron Majalisar Zartarwa ta jihar karo na 38 da aka gudanar ranar 12 ga watan Maris ba, lamarin da ya sake jawo muhawara kan halin da ake ciki na rikicin siyasa a gwamnatin jihar.

Taron, wanda gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya jagoranta, ya samu halartar mambobin majalisar zartarwa ta jihar. Sai dai rahotanni sun nuna cewa kujerar mataimakin gwamnan ta kasance babu kowa a kanta duk tsawon lokacin taron, duk da cewa an sanar da shi a hukumance.

Advertisement

Jami’an Tsaro Sun Kama Wata Mace Da Harsasai 884 A Kano

Masu sa ido kan harkokin siyasa a Kano na danganta rashin halartar taron da  sauyin siyasa da ya biyo bayan sauyin sheƙar  gwamnan jihar da wasu abokan siyasarsa suka yi zuwa jam’iyyar APC.

Advertisement

Rahotanni sun ce wasu daga cikin kwamishinonin da ba su bi wannan sauyi ba sun ajiye mukamansu da kansu, yayin da mataimakin gwamnan ya ci gaba da rike mukaminsa duk da cewa yana kuma jagorantar ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar a matsayin kwamishina.

Lamarin ya haifar da martani daga sassa daban-daban, inda wasu ke ganin cewa kasancewar mataimakin gwamna a wata jam’iyya dabam da gwamnan na iya kawo tsaiko wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

Advertisement

Haka kuma, batun ya sake tayar da muhawara kan yunkurin tsige shi da majalisar dokokin jihar ta fara aiwatarwa.

Wasu mazauna Kano sun bayyana ra’ayin cewa domin tabbatar da tafiyar da aiki cikin sauki a ma’aikatar ilimi mai zurfi, ya kamata mataimakin gwamnan ya yi tunanin ajiye mukamin kwamishina.

Advertisement

Zuwo lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa daga ofishin mataimakin gwamnan ko gwamnatin jihar da ta yi karin bayani kan dalilin rashin halartarsa a taron majalisar zartarwa na ranar 12 ga watan Maris.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending