Sports
UEFA Ta Yi Watsi Da Korafin Barcelona Kan Wasan Da Atletico Madrid Ta Doke Su
Hukumar UEFA ya yi fatali da ƙorafin da Barcelona ta shigar dangane da wani hukuncin alƙalin wasa da ya haifar da cecekuce, yayin wasan kwatafainal na gasar Zakarun Turai zagaye na farko.
Atletico Madrid ta doke Barcelona, amma sai Barca ta nemi a gudanar da bincike kan ƙwallon da ɗanwasan Atletico, Marc Pubill ya ɗauka da hannu a cikin da’irar 18 bayan da golansa ya bugo masa.
Pakistan Ta Ce Tana Ƙoƙarin Shawo Kan Amurka Da Iran Don Komawa Teburin Sulhu
Sai dai duk da taɓa ƙwallon da hannu, alƙalin wasa, Istvan Kovacs bai hukunta shi ba, balle ya bai wa Barca bugun ɗurme. Sannan alƙalin bidiyon VAR, Christian Dingert, shi ma bai zaɓi ya duba lamarin ba.
Barcelona ta koka kan cewa, kasancewar da ma Pubill yana da yalon kati a kansa, rashin duba lamarin da alƙalin VAR bai yi ba, abu ne da ya saɓa wa dokokin ƙwallo, kuma ya yi tasiri matuƙa kan ƙarshen wasan.
