Connect with us

News

Pakistan Ta Ce Tana Ƙoƙarin Shawo Kan Amurka Da Iran Don Komawa Teburin Sulhu

Published

on

images (5)

Gwamnatin Pakistan ta ce yanzu haka tana ci gaba da ƙoƙarin shawo kan ƙasashen Amurka da Iran domin komawa kan teburin tattaunawa da nufin samar da zaman lafiya a tsakaninsu, yunƙuri da ke zuwa kwana ɗaya bayan da Washington ta umarci sojojinta da su datse mashigin ruwan Hormuz.

Zauren da ke zaman cibiyar kafafen yaɗa labaran da suka bayar da rahotanni a kan zaman tattaunawar da aka yi tsakanin wakilan Amurka da na Iran a ƙarƙashin jagorancin ƙasarPakistan a birnin Islamabad. 12 ga Afrilu, 2026.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Harin Dakarun Sojin Sama Na Jilli Ya Sauka Ne Kan Maɓoyar ‘Yan Ta’adda

To bisa ga dukan alamu ɓangarorin biyu na da kyakkwar fatar ganin sun sake komawa kan teburin tattaunawa, kuma hujjar da ke nuni da hakan ita ce, yadda sama da sa’o’i 24 da sojojin Amurka suka fara aiwatar da barazanar rufe mashigin ruwan Hormuz har zuwa yanzu ba a ruwaito cewa an samu wata taƙaddama, ko jin ƙarar harbi balantana kai wa juna farmaki ba.

Advertisement

Bayanai sun ce a kowane lokaci daga yau, ɓangarorin biyu za su iya amincewa da sake komawa birnin Islamabad don fara tattaunawar.

A marecen jiya litinin, an jiyo shugaba Donald Trump na cewa yanzu haka akwai wasu manyan jami’an gwamnatin Iran masu ƙima’ da yake ci gaba da tattaunawa da su a sirrance duk da cewa bai ambaci sunayensu ba. Kuma mahukuntan Iran ba su ce komai ba a game da wannan iƙirari na shugaban Amurka.

Advertisement

Ko saboda me ake ɗaukar wannan batu na komawa kan teburin tattaunawa da muhimmanci?

Babu ɗaya daga cikin ɓangarorin da ya tabbatar da cewa zai koma Islamabad don ci gaba da tattaunawar, amma Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya fito fili ƙarara inda ya ce a nasu ɓangare ba wata matsala, zance ya rage a hannun mahukuntan ƙasar Iran, amma da sharaɗin cewa idan an koma, to za a tattauna ne a kan abin da Amurka ta gabatar tun da farko.

Advertisement

Ko akwai wani ƙoƙari da ƙasashen duniya ke yi don shawo kan Amurka ko Iran don ci gaba da tattaunawar?

Tun lokacin da aka ce Amurka ta ce ta rufe Mashigin Hormuz ake ganin cewa ta yi hakan ne domin tanƙwara sauran ƙasashen da ke amfana da wannan mashigi amma kuma suke ci gaba da nuna wa Iran sassauci.

Advertisement

China na daga cikin ƙasashen da ake ganin cewa rufe mashigin Hormuz zai sa dole ta sauya matsaya, ma’ana a maimakon ci gaba da mara wa mahukuntan Tehran baya, lokaci ya yi da ya kamata China ta yi musu matsin lamba domin su amince da ƙulla yarjejeniya da Amurka.

Kazalika akwai wasu manyan ƙasashe na Yammacin Duniya, domin ko a wannan talata, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jaddada kira ga Donald Trump da kuma Masoud Pezeshkian domin su gaggauta komawa teburin tattaunawa.

Advertisement

To amma a daidai lokacin da ake dakon ɓangarorin biyu su koma teburin tattaunawar, ita kuwa Amurka na ci gaba da datse mashigin Hormuz?

Ƙwarai kuwa, to sai dai bayanai na nuni da cewa duk da kasacnewarsa a rufe, jiragen ruwan dakon kaya da dama sun fice daga yankin tsakanin lahadi zuwa wannan talata.

Advertisement

Shugaban Amurka Trump na cewa adadin jiragen da suka fice da yardar Amurka za su kai 34, alƙaluman da Iran ta musanta. To sai dai alƙaluman Hukumar kula da zirga-zirga a kan tekunan duniya sun tabbatar da cewa jiragen ruwa guda biyu, ɗaya mai suna Christianna ya je ya sauke ton dubu 74 na masara a tashar ruwan Bandar Abas da ke Iran, sai kuma wani mai jirgin suna Elpis wanda ya je tashar jiragen ruwan Bushehr inda aka loda masa ton dubu 31 na sinadirin Methanol kafin ya fice ba tare da ya fuskanci wata tirjiya ba daga Amurka.

Ko meye illar ci gaba da kasancewar Hormuz a rufe ga duniya?

Advertisement

Akwai illoli, domin kuwa bayan share kusan kwanaki 40 Iran na hana wa jirage ficewa daga yankin, sai ga shi a yau Trump wanda ke ƙoƙarin buɗe Hormuz ne ya bayar da umarnin rufe shi baki ɗaya ba tare da yin la’akari da cewa kamfanoni da masana’antu a ƙasashen duniya na buƙatar makamashi da sauran sinadirai domin gudanar da ayyukansu ba.

To amma a ranar juma’a mai zuwa, ƙasashen duniya 40 da suka haɗa da Faransa da Birtaniya za su gudanar da taro don bayyana irin gudunmuwar da za su bayar wajen ganin cewa an sake buɗe mashigin na Hormuz.

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending