News
Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Tashi Daga Naira Tiriliyan 14.61 Zuwa Tiriliyan 159.28 Cikin Shekara Guda
Ofishin kula da basussukan Najeriya ya gabatar da wannan adadi, a ci gaba da rahotannin da yake bayarwa lokaci zuwa lokaci dangane da bashin da gwamnatin ƙasar ke ciyowa domin gudanar da manyan ayyuka.
Gwamnatin Najeriya ta tara yawan bashin kuɗaɗen ne daga watan Disambar shekarar 2024, zuwa Disambar 2025.
Ofishin ya ce bashin da Najeriya ta ciyo daga ƙasashen ƙetare ya kai naira tiriliyan 74.43 ya zuwa watan Disambar, wanda shi ne kashi 46.73 na basussukan da ake bin ƙasar.
Ko a watan Maris ɗin da ya gabata, sai da majalisar dokokin Najeriya ta amincewa shugaba Tinubu ciyo bashin dala biliyan 6.
Wani rahoton baya-bayan nan ya nuna cewa basukan da Najeriya ke ciyowa ya ƙaru a murabba’in farko na shekarar 2026 da muke ciki, bayan da gwamnatin ƙasar ta ciyo bashin Naira Triliyan 8.1 a cikin gida, wanda ya zarta tsarin dake ƙunshe a cikin kasafin ƙuɗinta na wannan shekara.
