Connect with us

News

Gwamnatin tarrayya Ta Janye Tuhumar Da Ta Ke Yiwa Malami Kan Ta’addanci

Published

on

malami
Tsohon Ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami

Mai gabatar da ƙara Akinlolu Kehinde ya sanar da matakin yayin zaman kotu na yau, inda ya ce za su ci gaba da tuhumar Malami a kan wasu batutuwa daban da suka shafi halarta kuɗaɗen haramun.

Bashin da ake bin najeriya ya tashi daga naira tiriliyan 14.61 zuwa tiriliyan 159.28 cikin shekara guda.

Advertisement

Lauyan Malami, Shaibu Aruwa ya shaidawa mai shari;a Joyce Abdulmalik cewar sun samu takardar yiwa tuhumar garambawul.

A watan Disambar 2025 ne gwamnatin ta zargi Malami da ɗan sa, da shirin aikata laifukan ta’addanci, saboda mallakar wasu muggan makami ba tare da izini ba.

Advertisement

Dama dai tun lokacin da aka gurfanar da Malami da ɗansa Abdul’aziz a gaban kotu, sun ƙi amincewa da zargin da ake musu na aikata laifukan ta’addancin, da a yanzu aka wanke su.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending