Connect with us

News

An Yi Jana’izar Mutane 13 Da Hatsarin Kwale-Kwale Ya Hallaka A Jigawa

Published

on

IMG 20260720 WA0041

An gudanar da jana’izar mutane 13 da suka rasa rayukansu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a yankin Malamawar Ƴandutse, da ke Ƙaramar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa.

Rahotanni sun nuna cewa kwale-kwalen na ɗauke da fasinjoji kusan 40 lokacin da ya kife yayin da suke tsallaka kogi. Yawancin fasinjojin na dawowa ne daga gonakinsu bayan kammala ayyukan noma.

Kotu Ta Bayar Da Belin Shugaban Miyetti Allah Bello Badejo Kan Naira Biliyan 2

Daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su akwai maza, mata da ƙananan yara. Jami’an ceto sun tabbatar da ceto mutane takwas da ransu, yayin da ake ci gaba da neman sauran da har yanzu ba a gano ba.

 

Ana fargabar adadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa, ganin cewa har yanzu akwai mutane da dama da ake zargin ruwa ya tafi da su.

Advertisement

 

Wannan lamari ya jefa al’ummar yankin cikin alhini, inda iyalai da ‘yan uwa ke zaman ɗar-ɗar suna jiran samun labarin sauran waɗanda suka ɓace.

 

Lamarin ya kuma sake bayyana buƙatar ƙara tsaurara matakan tsaron sufurin ruwa a ƙasar. Duk da cewa gwamnatin tarayya ta wajabta amfani da rigunan kariya (life jackets) ga masu amfani da jiragen ruwa tun a shekarar da ta gabata, rahotanni na nuna cewa har yanzu ba a aiwatar da wannan doka yadda ya kamata ba a wasu jihohi, ciki har da Jigawa.

Masu ruwa da tsaki sun bukaci hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da bin ƙa’idojin zirga-zirgar ruwa tare da wayar da kan al’umma kan muhimmancin amfani da rigunan kariya domin rage asarar rayuka a irin waɗannan hatsarori.

 

Advertisement

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending