News
Rahoton Samun Masu Bai Wa ‘Yan Ta’adda Bayanai a Hukumomin Tsaro Ya Jawo Cece-kuce
Jam’iyyun adawa a Najeriya sun bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta bincike tare da hukunta duk wani jami’i da aka tabbatar yana bai wa ‘yan ta’adda bayanai, bayan Fadar Shugaban Kasa ta ce akwai yiwuwar wasu masu taimaka wa ‘yan ta’adda sun kutsa cikin hukumomin tsaro.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, jam’iyyun adawar sun ce wannan furuci ya kara nuna irin kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta, tare da jaddada bukatar daukar matakan gaggawa domin dakile lamarin.
An Gano Gawa Ɗaya Bayan Kwale-Kwale Ya Kife Da Mutane 40 A Jigawa
Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Bolaji Abdullahi, ya ce zargin da ake yi na kutse cikin hukumomin tsaro bai kamata ya tsaya a matsayin magana kawai ba, illa ya kamata gwamnati ta gudanar da cikakken bincike domin gano masu hannu a ciki tare da hukunta su bisa doka.
Hakazalika, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Rufus Aiyenigba, ya ce idan gwamnati ta tabbatar da zargin, wajibi ne ta kamo tare da gurfanar da duk wanda aka samu yana bai wa ‘yan ta’adda goyon baya ko bayanai.
Ya yi gargadin cewa jinkiri wajen daukar matakin da ya dace na iya kara ta’azzara matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar.
Wannan cece-kuce ta biyo bayan kalaman Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Daniel Bwala, wanda ya ce akwai yiwuwar wasu masu alaka da ‘yan ta’adda sun kutsa cikin wasu sassan hukumomin tsaro.
Sai dai Bwala ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da daukar matakan da suka dace domin bincike da magance duk wani barazana ga tsaron kasa.
