Connect with us

News

RITAYAR DOLE: Darakta Ya Kai Gwamnan Kano, Babban Lauyan Gwamnati Da Hukumar JSC Kotu

Published

on

kotu

Wani Darakta mai riƙon muƙamin Sashen Hulɗa da ‘Yan Jaridu da Kididdiga a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano, Muzambilu Ado, ya shigar da ƙara a Kotun Ƙwadago ta Ƙasa, inda yake ƙalubalantar matakin da Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta ɗauka na tilasta masa yin ritaya.

A cikin ƙarar, Ado ya buƙaci kotun ta soke umarnin ritayar dole da aka yi masa, tare da umartar a biya shi diyyar Naira miliyan 100 bisa abin da ya bayyana a matsayin ɓata masa suna da kuma tauye masa haƙƙinsa.

An Yi Jana’izar Mutane 13 Da Hatsarin Kwale-Kwale Ya Hallaka A Jigawa

JSC ta sanar da ritayar Ado ne bayan wani bincike da ta gudanar, inda ta ce an gano rashin daidaito a takardun karatunsa, ciki har da zargin sauya bayanai da kuma amfani da takardun shaidar karatu da ba su da inganci wajen samun aiki.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Baba Jibo Ibrahim, ya fitar a ranar 6 ga Yulin 2026, JSC ta ce matakin ya biyo bayan rahoton kwamitin bincike da ya gano kura-kurai a takardun karatun Ado, tare da zarginsa da shiga Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Ƙasa ba tare da izinin hukuma ba.

Sai dai a cikin ƙarar da ya shigar, Ado ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, yana mai cewa an ɗauke shi aiki tun shekarar 2006 da takardar Diploma a Nazarin Mulki daga Kaduna Polytechnic, kuma bai taɓa gabatar da takardar HND a matsayin cancantarsa ba.

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa ya samu Digirin Lauya (LL.B) daga Jami’ar Imperial da ke Sudan a shekarar 2022, yana mai cewa jami’ar ta tabbatar wa JSC cewa ya kammala karatunsa bisa ƙa’ida.

Ado ya ƙara da cewa ba a ba shi damar kare kansa ba kafin a ɗauki matakin ritayar dole, domin ba a miƙa masa kwafin koken da aka yi a kansa ko kuma a gayyace shi ya kare kansa kamar yadda dokokin aikin gwamnati suka tanada.

Dangane da batun shiga Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Ƙasa, ya ce ya nemi izini tare da wasu ma’aikata huɗu, amma ba a sanar da shi ko an amince da buƙatarsa ko an ƙi ba.

A nasa ɓangaren, mai magana da yawun JSC, Baba Jibo Ibrahim, ya ce hukumar ba za ta yi cikakken bayani kan lamarin ba saboda yana gaban kotu.

Sai dai ya bayyana cewa binciken ya samo asali ne daga koken da wani ma’aikacin shari’a, Sani Manzo, ya gabatar, inda aka buƙaci a tantance sahihancin takardun karatun Ado.

Ya ce Makarantar Koyon Aikin Lauya ta yi ƙoƙarin tantance takardun ta hanyar tuntuɓar Jami’ar Imperial ta adireshin imel da aka gabatar, amma saƙonnin sun gaza isa, lamarin da ya ƙara jefa shakku kan ingancin takardun.

Advertisement

Baba Jibo ya kuma ce Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Ƙasa daga bisani ta soke damar Ado ta ci gaba da karatu bayan ta ce bai gabatar da isassun hujjoji da za su tabbatar da sahihancin takardunsa ba.

Jaridar Inda Ranka ta gano cewa waɗanda aka shigar da ƙarar sun haɗa da Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano (JSC), Gwamnan Jihar Kano da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano.

Ana sa ran Kotun Ƙwadago ta Ƙasa za ta fara sauraron shari’ar domin yanke hukunci kan sahihancin matakin ritayar dole da kuma buƙatun da mai ƙarar ya gabatar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending