News
Dakarun Soji Sun Kama Ƴan Ƙasar Waje Biyu Da Su Ke Kai Wa Yan Boko Haram Makamai A Borno
Dakarun operation HADIN KAI sun kama wani ɗan ƙasar Sudan da a ke zargi ɗan ta’adda ne tare da wata mata da ta ce ita ƴar ƙasar Ghana ce, a wani samame da su ka kai a yankin Lassa, Dille da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
An gudanar da samamen ne da misalin karfe 11:48 na safe ranar 19 ga Yuli, 2026, inda dakarun Bataliya ta 115 su ka kama Musa Fashir, mai shekaru 32, ɗan ƙasar Sudan, wanda ake zargin yana da alaƙa da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda kuma yana taimaka musu.
RITAYAR DOLE: Darakta Ya Kai Gwamnan Kano, Babban Lauyan Gwamnati Da Hukumar JSC Kotu
Haka kuma, dakarun sun kama Mary Florence, mai shekaru 36, wadda ta bayyana kanta a matsayin baƙuwar ‘yar ƙasar Ghana da ta shiga Najeriya ba bisa ƙa’ida ba. Jami’an tsaro sun ce ana ci gaba da bincike kan sahihancin bayananta da kuma dalilin kasancewarta a yankin.
A halin yanzu, waɗanda aka kama na hannun sojoji, inda ake yi musu tambayoyi domin tabbatar da asalinsu da kuma gano ko suna da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci ko wasu masu aikata manyan laifuffuka.
Dakarun sun ce nasarar ta nuna yadda ayyukan tattara bayanan sirri ke taimakawa wajen dakile shigowar mayaƙan ƙasashen waje da masu taimaka wa ƴan ta’adda. Rundunar ta kuma buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin arewa maso gabas.
