Connect with us

News

An Sace Shugaban Makaranta Da Dalibai Masu  Rubuta Jarabawar NECO A Kogi

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata makarantar sakandare ta gwamnati da ke Odo-Ekina a Jihar Kogi, inda suka sace shugaban makarantar, wani ma’aikacin wucin gadi na Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare (NECO), da wasu ɗalibai yayin da ake rubuta jarabawar NECO.

Advertisements
Advertisements

Jaridar the guardian ta ruwaito ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da ɗalibai ke tsaka da rubuta jarabawa. An ce maharan sun shiga makarantar, lamarin da ya haddasa firgici tsakanin ɗalibai da malamai, kafin su tafi da waɗanda suka sace zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Advertisements

An sace Shugaban Makaranta Da Dalibai Masu  Rubuta Jarabawar NECO A Kogi

Advertisements
Advertisements

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’anta sun fara aikin ceto nan take bayan samun rahoton harin. Rundunar ta kuma bayyana cewa an ceto ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace, yayin da ake ci gaba da neman sauran mutanen.

Har yanzu dai ba a bayyana adadin ɗaliban da aka sace a hukumance ba, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike da kuma farautar waɗanda suka aikata laifin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending