Connect with us

News

“Boka Ne Ya Umarce Ni Na Kashe Ƙanwar Mahaifina Da ’Ya’yanta Shida” — Umar Auwalu A Kotu

Published

on

IMG 20260715 WA0018

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba ta 11, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi wa Umar Auwalu, Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu, kan zargin kisan Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Ciranci da ke Kano.

A zaman kotun na ranar Laraba, Umar Auwalu mai shekaru 23, yayin da yake kare kansa, ya shaida wa kotu cewa shi kaɗai ne ya aikata kisan ƙanwar mahaifinsa, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida a watan Janairun 2026. Ya ce wani boka kuma mai sayar da maganin gargajiya mai suna Thomas ne ya ba shi wani turare tare da umartarsa ya ci gaba da aikata irin waɗannan laifuka.

Zaɓen 2027: Kungiyoyin Fararen Hula Sun Bukaci Dakatar Da Gangamin Siyasa A Kano

Umar ya kuma bayyana cewa waɗanda ake tuhuma tare da shi, Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu, ba su da hannu a aikata laifin. A cewarsa, ya ambaci sunayensu ne bayan da ya fuskanci azaba a hannun jami’an ’yan sanda bayan kama shi.

Lauyoyin gwamnati, ƙarƙashin jagorancin Barista Safiya Yalwati da Barista Zaharaddeen Hamisu Kofar Mata, sun gabatar da jami’in binciken ’yan sanda, Kofural Aliyu Jamilu, a matsayin shaida. Haka kuma, lauyoyin masu kare waɗanda ake tuhuma sun gabatar da shaidunsu gaban kotu.

Mai Shari’a Nasiru Saminu ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga Yuli, 2026, domin ci gaba da karɓar shaidu da sauraron ɓangarorin da ke ƙara.

Advertisement

Ana zargin cewa a ranar 17 ga Janairu, 2026, an kashe Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a gidansu da ke Dorayi Ciranci, lamarin da ya girgiza al’ummar Jihar Kano. Bayan binciken da ’yan sanda suka gudanar, an kama Umar Auwalu tare da wasu mutum biyu bisa zargin hannu a kisan.

Tun da farko an gurfanar da su a Kotun Majistare da ke Nomansland kan tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da haɗa baki, kisan kai, fashi da makami da kuma fyade. Daga bisani, bayan nazarin da Daraktan Hukumar Gurfanar da Masu Laifi (DPP) ya yi, an mayar da shari’ar zuwa Babbar Kotu inda aka sake gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda tara. Yayin da Umar ya amsa wasu daga cikin zarge-zargen, sauran waɗanda ake tuhuma biyu sun musanta aikata dukkan laifukan da ake zarginsu da su.

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending