Sports
FIFA Ta Ci Tarar Najeriya
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, ta ci tarar Najeriya da Jamhuriyar Congo sakamakon laifukan da suka shafi rashin bin dokokin tsaro a wani wasa da suka fafata a watan Nuwamba.
A cikin sanarwar da kwamitin ladabtarwa na FIFA ya fitar, an ce Najeriya ta karya dokokin tsaro bayan wasu magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar, Super Eagles, sun jefa abubuwa cikin fili yayin wasan.
Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranakun Komawa Makaranta
Saboda haka, FIFA ta ci tarar Najeriya kudi Swiss franc 1,000 bisa karya sashe na 17 da kuma sashe na 12 na dokokinta.
A nata bangaren, Congo ta fuskanci tara mafi tsauri ta Swiss franc 5,000 bayan da magoya bayanta suka yi amfani da fitilu wajen haskaka fuskar ‘yan wasan Najeriya, lamarin da ya saba wa dokokin FIFA.
Wasan dai ya gudana ne a ƙasar Morocco, inda Najeriya ta yi rashin nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Bayan wasan, kocin Najeriya, Eric Chelle, ya zargi tawagar Congo da aikata wasu abubuwa da bai kamata ba, ciki har da zargin amfani da tsafi.
