News
Sama Da Yan Najeriya 700 Har Yanzu Na Makale A Kasar Afirka Ta Kudu

Sama da ‘yan Najeriya 700 ne har yanzu ke makale a ƙasar Afirka ta Kudu, duk da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware kuɗaɗen gudanar da aikin kwaso zuwa gida tun kusan makonni biyu da suka gabata.
Rahotanni sun nuna cewa tsaiko a tsarin gudanar da harkokin gwamnati ne ya hana isar da kuɗaɗen ga kamfanin jiragen sama na Air Peace, lamarin da ya jinkirta ci gaba da aikin ceto ‘yan ƙasar da ke cikin fargabar hare-haren ƙyamar baƙi (Xenophobia).
Ƴansanda Sun Ceto Yara Huɗu, Sun Kama Mata Biyu Kan Zargin Safarar Yara A Neja
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zanga-zangar ƙungiyoyin masu adawa da baƙi daga ranar 30 ga Yuni, abin da ya ƙara tayar da hankalin ‘yan Najeriya da sauran baƙi da ke zaune a Afirka ta Kudu.
Bayanan da jami’ai daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM) da kuma Babban Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Afirka ta Kudu suka bayar sun nuna cewa Air Peace ta ƙi tura jiragenta har sai gwamnati ta tabbatar da biyan kuɗin aikin.
A cewar jami’an, kusan ‘yan Najeriya 1,000 ne suka yi rajistar son dawowa gida. Sai dai mutum 258 ne kawai aka kwaso a jirgi na farko ranar 11 ga Yuni, yayin da wasu mutum 66 suka dawo Legas a ranar 24 ga Yuni ta jirgin ValueJet, bayan wani mai hannu da shuni ya ɗauki nauyin tikitinsu.
