News
Ƴansanda Sun Ceto Yara Huɗu, Sun Kama Mata Biyu Kan Zargin Safarar Yara A Neja

Rundunar Ƴansandan Jihar Neja ta ce ta kama wasu mata biyu da ake zargi da safarar yara da kuma aikata ayyukan tsafi, tare da ceto yara huɗu masu shekaru tsakanin huɗu zuwa bakwai a garin Suleja.
Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa jami’an sashen tattara bayanan sirri ne suka kama Mrs. Promise Chukwudi mai shekaru 68 da Mrs. Suzanna Onojekwo mai shekaru 62, bayan wani samame da suka kai wani gida da ke bayan tsohon ofishin NEPA a ranar 3 ga Yunin 2026.
Amurka Da Iran Sun Amince Su Dakatar Da Hare-hare Don Cigaba Da Tattaunawa
A cewarsa, an tarar da yaran ne a gidan Suzanna, inda waɗanda ake zargin suka yi ikirarin cewa iyayensu ne suka ba su yaran domin reno da ɗaukar su a matsayin ‘ya’ya. Sun ce yaran sun fito ne daga yankin Karim-Lamido na ƙaramar hukumar Gassol da ke Jihar Taraba tsakanin watan Nuwamban 2025 zuwa Fabrairun 2026.
Sai dai binciken ƴansanda ya nuna sabanin wannan bayani, bayan da wasu iyaye daga Abuja da jihohin Nasarawa da Benue suka bayyana suna neman yaran, suna masu cewa ‘ya’yansu ne.
Sanarwar ta ce ɗaya daga cikin matan ta bayyana cewa a baya ta kasance mai kula da cibiyar marayu mai suna Precious Promise Nursery, Primary and Orphanage Home, wadda ta fara aiki tun shekarar 2022 kafin ta sake buɗe ta a ƙarshen shekarar 2025. Ta kuma ce tana da lasisin yin magungunan gargajiya.
Ƴansandan sun ce yayin binciken gidan, sun gano wani wuri da ake zargin ana gudanar da tsafi, inda aka samu ƙwanyar dabbobi, gashin tsuntsaye, tufafi masu kala daban-daban da wasu kayayyakin gargajiya.
Rundunar ta ce an tura waɗanda ake zargin zuwa hedikwatar Ƴansanda da ke Minna domin ci gaba da bincike, yayin da aka miƙa yaran ga hukumar kula da haƙƙin yara domin kula da su har sai an kammala tantance iyayensu.
Haka kuma, rundunar ta tabbatar da cewa an gurfanar da matan a gaban kotu domin su fuskanci tuhumar da ake yi musu.
