Connect with us

News

Fassarar Jawabin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu Na Ranar Dimokradiyya

Published

on

1781261865119

SAKON SHUGABA BOLA AHMED TINUBU A RANAR DIMOKURAƊIYYA TA 12 GA YUNI, 2026

 

Advertisement

‘Yan uwana ’yan Najeriya,

A yau muna bikin dimokuraɗiyya da kuma juriyar ruhin ɗan Najeriya. Tsawon shekaru 27 a jere tun daga ranar 29 ga Mayu, 1999, al’ummarmu ta ci gaba da zaɓar shugabanninta ta hanyar akwatin zaɓe, tana ganin sauyin mulki cikin lumana, tare da warware sabani a kotuna da majalisun dokoki maimakon ta hanyar tashin hankali.

Advertisement

Dimokuraɗiyyarmu ba cikakkiya ba ce, amma tamu ce. Don haka wajibi ne mu ci gaba da kare ta tare da ƙarfafa ta.

A kwanaki masu zuwa, jihohin Ekiti da Osun za su gudanar da zaɓe. Ina kira ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), jami’an tsaro da dukkan masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa an gudanar da waɗannan zaɓuka cikin lumana da gaskiya. Dimokuraɗiyya tana raunana idan jama’a suka rasa amincewa da tsarin zaɓe.

Advertisement

Ga Majalisar Tarayya, Bangaren Shari’a, ’Yan Jarida da Kungiyoyin Farar Hula: ku ne ginshiƙan da ke kare jamhuriyarmu. Ku ci gaba da sukar gwamnati idan ya dace, ku yi sabani da ni idan kuna da hujja, amma kada ku daina yarda da Najeriya.

Ga matasanmu, Najeriya ita ce gidanku kuma makomarku. Ku gina ta a nan, ku kirkiri sababbin fasahohi a nan, ku yi aiki a nan, ku kuma kada kuri’a a nan. Manyan ƙasashe ba su samu ci gaba ba saboda mutanen da suka gudu daga matsaloli, sai dai saboda waɗanda suka tsaya suka warware su.

Advertisement

Gobara Ta Kone Fiye Da Rumfuna 70 A Kasuwar Kingsway Da Ke Kano

Ina miƙa gaisuwa ta musamman ga dakarunmu, jami’an ’yan sanda da jami’an tsaro saboda sadaukarwar da suke yi. Haka kuma ina godiya ga sarakunan gargajiya, malamai da shugabannin al’umma saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da sulhu.

Advertisement

A yau muna tunawa da juriyar ’yan Najeriya da suka ƙi yin kasa a gwiwa wajen kare ’yanci da dimokuraɗiyya. Muna girmama waɗanda suka fuskanci tsangwama, kurkuku, gudun hijira har ma da rasa rayukansu domin al’ummomin gaba su more dimokuraɗiyya.

Muna kuma tunawa da shugabannin ƙwadago, ’yan jarida, masu fafutuka, ɗalibai, mata, ƙwararru, shugabannin siyasa da sojoji da suka taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da dimokuraɗiyya a ƙasarmu.

Advertisement

Duk da cewa wannan shekarar ta zo da alhini sakamakon sace yaranmu a jihohin Oyo da Borno, muna ci gaba da addu’ar dawowarsu lafiya. Domin dimokuraɗiyya ba za ta yi ƙarfi ba idan babu tsaro.

Saboda haka gwamnatinmu ta ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro tare da amincewa da lɗaukar sabbin jami’an ’yan sanda sama da 50,000 da kuma dubban sababbin sojoji. Kasafin kuɗin shekarar 2026 ya ware Naira tiriliyan 5.41 domin tsaro, mafi girma a tarihin Najeriya.

Advertisement

Mun ci gaba daga matakin horaswa tare da ƙasashen abokan hulɗarmu kamar Amurka da Faransa zuwa matakin kai farmaki daidai kan wuraren da ’yan ta’adda suke. A yankin Arege da ke Jihar Borno, mun lalata babban sansanin jagorancin ISWAP.

Yawan mutanen da ake kashewa sakamakon ta’addanci ya ragu da kashi 81 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar 2015. Fiye da ’yan ta’adda 13,000 aka kawar a cikin shekara guda da ta gabata.

Advertisement

Sai dai har yanzu muna buɗe ƙofa ga waɗanda suka yanke shawarar mika wuya. Tun daga shekarar 2023, sama da mutane 124,000 daga cikin mayaƙa da iyalansu sun ajiye makamansu ta hanyar shirin Operation Safe Corridor.

Ga ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta’addanci: ku mika wuya ko ku fuskanci cikakken ƙarfin gwamnatin Najeriya. Wannan damar ba za ta kasance a buɗe har abada ba.

Advertisement

A irin wannan lokaci, bai kamata mu riƙa ɗora laifi kan wata ƙabila ko wani yanki ba. Laifi ba shi da ƙabila. Dole ne mu kasance a haɗe domin makiyan Najeriya za su zama tarihi nan ba da jimawa ba.

Ranar 12 ga Yuni tana da matsayi na musamman a tarihin ƙasarmu. Ba wai kawai ranar zaɓe ba ce, rana ce da ta nuna yiwuwar gina Najeriya guda ɗaya.

Advertisement

Muna tunawa da Marigayi Cif M.K.O. Abiola wanda ya samu karɓuwa daga kowane sashe na Najeriya ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba. Muna kuma tunawa da Marigayiya Kudirat Abiola da sauran jaruman dimokuraɗiyya.

Muna tunawa da Gani Fawehinmi, Bola Ige, Alfred Rewane, Abraham Adesanya, Anthony Enahoro, Balarabe Musa, Dan Suleiman, Beko Ransome-Kuti, Frank Kokori, Arthur Nwankwo, Chima Ubani, Shehu Musa Yar’Adua da sauran jarumai maza da mata da suka sadaukar da kansu domin tabbatar da ’yancin da muke morewa a yau.

Advertisement

Jaruman 12 ga watan Yuni sun samar mana da ’yancin siyasa. Nauyin da ke kanmu yanzu shi ne samar da ’yancin tattalin arziki.

Dimokuraɗiyya dole ne ta bayyana a rayuwar jama’a, a damar da matasa ke samu, a bunƙasar noma, a ci gaban ’yan kasuwa da kuma mutuncin ma’aikata.

Advertisement

Gyaran tattalin arzikin da muka fara bai kasance domin sauƙi ba, sai dai domin ya zama wajibi.

Tun daga shekarar 2023, waɗannan gyare-gyare sun dawo da kwanciyar hankali ga tattalin arzikin ƙasa. Kuɗaɗen shiga na gwamnati sun ƙaru, an rage almundahana, an ƙara gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a, kuma amincewar masu zuba jari ta dawo.

Advertisement

Zuba jari ya ƙaru a fannoni kamar noma, makamashi, masana’antu, fasaha, ma’adinai, sufuri da masana’antun kirkira.

Haka kuma ƙarfin tace mai a cikin gida ya ƙaru, wanda ke taimakawa wajen ƙarfafa tsaron makamashi da rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

Advertisement

Lokacin da muka hau mulki, bangaren wutar lantarki na fama da matsaloli masu yawa. Don magance wannan matsala, na rattaba hannu kan Dokar Wutar Lantarki da ta bai wa jihohi damar samarwa, rabawa da kuma sarrafa wutar lantarki.

Hukumar Kula da Samar da Wutar Lantarki ta Ƙasa tana aiki don rage matsalar rashin mita, tare da shirin tara Naira tiriliyan 4 domin biyan tsofaffin basussuka a bangaren.

Advertisement

A yankunan karkara, an samar da wutar lantarki ta hanyar mini-grid da sauran hanyoyi domin hidimta wa al’ummomi, jami’o’i, kasuwanni da asibitoci.

Domin wutar lantarki hakki ne da ya kamata kowane ɗan Najeriya ya mora.

Advertisement

Duk da nasarorin da aka samu, har yanzu muna sane da cewa ’yan Najeriya da dama suna fuskantar matsin rayuwa.

Saboda haka muna mai da hankali wajen rage hauhawar farashi, ƙara samar da abinci, samar da ayyukan yi, da inganta rayuwar jama’a.

Advertisement

Mun fara fita daga yanayin rashin tabbas zuwa kwanciyar hankali. Mataki na gaba shi ne hanzarta ci gaba tare da tabbatar da cewa kowane gida, kowace al’umma da kowane yanki ya amfana da shi.

Domin dimokuraɗiyya dole ne ta bayyana a aljihun jama’a.

Advertisement

Domin tabbatar da cewa jama’a suna jin tasirin dimokuraɗiyya kai tsaye, gwamnatinmu ta himmatu wajen tabbatar da cikakken ’yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.

Matsalolin rashin tsaro da wasu kalubalen ci gaba sun samo asali ne daga rushewar tsarin mulki a matakin ƙasa. Saboda haka Ajandar Sabunta Fata tana nufin tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya ya amfana da gwamnati.

Advertisement

Muna girmama Marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua saboda hangen nesa da gudummawar da ya bayar wajen gina Najeriya mai haɗin kai.

A saboda haka, gwamnatin tarayya ta amince da sauya sunan Cibiyar Nazarin Man Fetur da ke Kaduna zuwa Jami’ar Kimiyyar Kasa da Fasahar Injiniya ta Janar Shehu Musa Yar’Adua.

Advertisement

Haka kuma na amince da karrama wasu fitattun ’yan Najeriya da suka fuskanci tsangwama, kurkuku, gudun hijira da wahalhalu domin kare dimokuraɗiyya da suka hada da;

Barista Ayoka Lawani

Advertisement

Tunde Fagbenle

Oladele Alake

Advertisement

Olatunji Bello

Louis Odion

Advertisement

Segun Babatope

Sam Omatseye

Advertisement

Sir Ademola Osinubi

Bola Bolawole

Advertisement

Lade Bonuola

Femi Kusa

Advertisement

Debo Adeniran

Cif Ayo Opadokun

Advertisement

Cif Ralph Obiora

Ose Osayande

Advertisement

Barista Osa Director

Farfesa Sylvester Odion-Akhaine

Advertisement

Marigayi Dakta Arthur Nwankwo

Dakta Osagie Obayuwana

Advertisement

Dakta Joe Okei-Odumakin

Barista Titus Mann

Advertisement

Joe Igbokwe

Richard Akinnola

Advertisement

Marigayi Ben Charles-Obi

George Mbah

Advertisement

Dakta Niran Malaolu

Manjo Janar Ishola Williams (Mai Ritaya)

Advertisement

Femi Aborisade

Jenkins Alumona

Advertisement

Gbemiga Ogunleye

Muyiwa Adekeye

Advertisement

Babajide Kolade-Otitoju

Ike Okonta

Advertisement

Haka Kuma Muna Girmama Sojojin Da Suka Taka Rawa A Gwagwarmayar 12 ga Yuni da suka hada da;

Manjo Janar M. A. Garba

Advertisement

Birgediya Janar Lawal Ja’afaru Isa

Kanal Umar Farouk Ahmed

Advertisement

Kanal Sambo Dasuki

Kanal Lawan Gwadabe

Advertisement

Birgediya Janar Jonathan Ndam Temlong

Kanal Musa Shehu

Advertisement

Manjo Janar Chris Eze

Manjo Janar Harris Dzarma

Advertisement

Kanal Isa Jibrin

Manjo Janar Joseph Oshanupin

Advertisement

Kanal Olusegun Oloruntoba, Olugbede na Masarautar Gbede

Laftanar Kanal Happy Kefas Bulus

Advertisement

Kanal J. Okai

Kanal Emmanuel Ndubueze

Advertisement

Laftanar Kanal Yakubu Mu’azu

Birgediya Yahaya Abubakar, Etsu Nupe na yanzu, wanda tuni yake da lambar yabon ƙasa ta CFR.

Advertisement

Za a fitar da cikakken jerin sunayen waɗanda za a karrama tare da lambobin yabon ƙasa da za a ba su a cikin kwanaki masu zuwa.

Yan uwana ’yan Najeriya,

Advertisement

Shekaru 27 da suka gabata, mutane da yawa sun yi shakku cewa dimokuraɗiyya za ta dawwama a Najeriya saboda bambance-bambancenmu.

A yau kuwa, waɗannan bambance-bambancen ne suke ƙarfafa dimokuraɗiyyarmu.

Advertisement

Hanyar gaba ba mai sauƙi ba ce. Amma 12 ga Yuni tana tunatar da mu cewa ’yan Najeriya ba sa karyewa. Za mu iya lanƙwasawa, za mu iya zubar da jini, amma ba za mu rushe ba.

Mu sabunta alkawarinmu cewa wahalhalun jarumanmu na baya ba za su tafi a banza ba, kuma mulkin jama’a, na jama’a kuma domin jama’a ba zai gushe daga wannan ƙasa ba.

Advertisement

Allah Ya albarkaci jaruman dimokuraɗiyyarmu.

 

Advertisement

Allah Ya albarkaci Tarayyar Najeriya.

 

Advertisement

Allah Ya ci gaba da albarkatar mu baki ɗaya.

 

Advertisement

Barka da Ranar Dimokuraɗiyya.

 

Advertisement

BOLA AHMED TINUBU, GCFR

Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Tarayyar Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending