News
Peter Obi Ya Bukaci INEC Da Ta Wallafa Bayanan Shaidar Kammala Karatun ‘Yan Takara
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta bayyana wa jama’a takardun shaidar kammala karatu da sauran takardun cancantar da dukkan ’yan takara ke miƙawa kafin zaɓe.
Obi ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, inda ya ce yin hakan zai ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amana a tsarin zaɓen Najeriya, tare da bai wa jama’a damar tantance cancantar masu neman shugabanci.
Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Saboda Laifin Satar Amsa Lokacin Jarabawa
Ya ce yayin da yake cike fom ɗin tsayawa takara na INEC, ya lura cewa ana tambayar ɗan takara ko kotu ta taɓa ayyana shi a matsayin mai tabin hankali ko kuma wanda ba ya cikin cikakkiyar lafiyar hankali.
A cewarsa, wannan ya sa ya yi tunanin ko shugabannin Najeriya na nuna halayen shugabanci irin na mutanen da ke da cikakkiyar basira da hangen nesa, musamman idan aka yi la’akari da irin matsalolin tsaro da tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.
Obi ya ce abin da ya kamata ya fi ɗaukar hankalin shugabanni a yanzu shi ne ceto rayuka da magance matsalolin tsaro, yunwa da talauci, maimakon shagaltuwa da siyasa.
Ya ƙara da cewa akwai wata tambaya a cikin fom ɗin INEC da ke neman sanin ko ɗan takara ya taɓa gabatar da takardar shaidar bogi ga hukumar.
Saboda haka, ya ce ya dace INEC ta wallafa takardun karatu da sauran bayanan cancantar da ’yan takara suka gabatar domin jama’a su tantance su da kansu.
“Bayyana waɗannan bayanai zai ƙarfafa gaskiya, inganta dimokuraɗiyya da kuma ƙara wa jama’a kwarin gwiwa kan tsarin zaɓe,” in ji Obi.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
