Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Sake Fasalin Tsarin JSS Da SSS A Makarantun Sakandare

Published

on

FB IMG 1762488671790
Advertisements
ads

Gwamnatin tarayya ta yi umarnin sauya tsarin karatu a Najeriya, sakamakon gano cewa fiye da yara miliyan 20 ƴan makarantar firamare sunabarin makarantar tun kafin su kai ga matakin sikandire.

Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, shi ne ya bayyana hakan a yau Talata, a wajen ƙaddamar da kwamitin sanya idanu na ma’aikatar shirin ilimin bai ɗaya na ƙasa a birnin tarayya Abuja.

Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Saboda Laifin Satar Amsa Lokacin Jarabawa ‎

Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa Najeriya dai tana gudanar da tsarin ilimi na shekaru 6-3-3-4, wanda ya ƙunshi shekaru shida na firamare, shekaru uku a ƙaramar sikandire, shekaru uku a babbar sikandire, sai kuma ma fi ƙarancin shekaru hudu a matakin gaba da sikandire.

Tuni ya bayyana cewa tsarin da ya raba babba da ƙaramar sikandire bai yi wanitasiri ba, kuma ya bayar da gudumawa matuƙa gaya wajen ƙaruwar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ya kuma ƙara da cewa ƙudirin da ya kawo raba makarantun zuwa kashi biyu ya lalata damar samun ilimi, sakamakon cikowar ƙananun makarantun sikadndire ba tare da cike manyan makarantun ba.

Advertisement

Alausa ya ce kimanin yara miliyan 24 ne su ka shiga zuwa makarantun firamare, amma iya miliyan hudu ne kawai su ka kammala zuwa matakin sikandire. Inda adadin miliyan 20 su ka yi watsi da zuwa makarantar baki ɗaya.

A ƙarshe ministan ya bayyana cewa za a gabatar da buƙatar rushe tsarin karatun a zaman majalisar ƙolin ilimi ta ƙasa nagab, domin a yi duba kan lamarina hukumance.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending