News
An Tsinci Wata jinjira A Masallacin Jumma’a A Argungu
An tsinci wata jinjira da aka haifa kimanin makonni uku da suka gabata a Masallacin Sheikh Musa Fakkai da ke garin Argungu, Jihar Kebbi.
Jami’ar Hukumar Hisbah ta Ƙaramar Hukumar Argungu, Hajiya Rabi Ahmed, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’an hukumar sun samu rahoton jaririyar ne a safiyar Asabar daga jami’an tsaron farin kaya.
An Gano Wuraren Hakar Ma’adinai 374 Ba Bisa Ka’ida Ba A Jihohi 17 — Gwamnatin Tarayya
A cewarta, bayan samun rahoton, jami’an Hisbah sun isa masallacin, inda suka ɗauki jaririyar tare da miƙa ta ga ƙungiyar Mar’atussaliha da ke da cibiya a Argungu, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Mariya Mera.
Ta ce jaririyar ta bambanta da wasu daga cikin yaran da ake samu a irin wannan yanayi, domin an same ta sanye da kaya masu yawa, tare da kayan kwalliya, man shafawa da sauran abubuwan da ake amfani da su wajen kula da jarirai.
Hajiya Rabi ta ce hakan na iya nuna cewa an kula da jaririyar kafin a ajiye ta a masallacin, tana mai cewa har yanzu ba a gano iyayenta ko dalilin da ya sa aka bar ta a wajen ba.
Ta ƙara da cewa ƙungiyar ta nemi tallafi daga Ƙaramar Hukumar Argungu, amma ba ta samu ba, lamarin da ya sa suka garzaya fadar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammed Mera, inda aka ba su tallafin gaggawa domin samar da abubuwan da jaririyar ke buƙata.
Hajiya Rabi ta yi kira ga iyaye, musamman mata, da su ƙara kula da ‘ya’yansu mata domin gano matsalolin da za su iya fuskanta tun da wuri.
Ta kuma yi kira ga Ma’aikatar Mata da sauran masu ruwa da tsaki da su riƙa tallafa wa ƙungiyoyin da ke kula da irin waɗannan jarirai, musamman wajen samar da magunguna, sabulu, abinci da sauran kayan amfani na yau da kullum.
