Connect with us

News

An Gano Wuraren Hakar Ma’adinai 374 Ba Bisa Ka’ida Ba A Jihohi 17 — Gwamnatin Tarayya 

Published

on

IMG 20260927 WA0027

Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano wuraren haƙar ma’adinai 374 da ake gudanar da ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a jihohi 17 na Najeriya tsakanin watan Maris na 2024 zuwa Agustan 2026.

Ministan Ma’adanai da Ƙarafa, Dele Alake, ne ya bayyana hakan, inda ya ce daga cikin wuraren da aka gano, an samu nasarar rufe 108.

Mota Ta Afka Ma’ajiyar Tukwanan Gas A Abuja

Alake ya bayyana cewa jami’an gwamnati sun kama mutane 743 da ake zargi da hannu wajen gudanar da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a wuraren da aka gano.

Ya ce daga cikin waɗanda aka kama, an gurfanar da mutane 430 a gaban kotu, a ƙarƙashin shari’o’i 165 da suka shafi ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Ministan ya ƙara da cewa kawo yanzu kotuna sun yanke wa mutane biyar hukunci kan laifukan da suka shafi haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Advertisement

Ya ce gwamnati na ci gaba da amfani da jami’an Mining Marshals wajen gano wuraren da ake gudanar da ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, tare da ɗaukar matakan shari’a kan waɗanda ake zargi da karya dokokin ƙasa.

Gwamnatin Tarayya ta sha yin gargadi kan illolin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, musamman yadda ayyukan ke iya haifar da lalacewar muhalli, gurɓacewar ruwa da kuma barazana ga tsaron ƙasa.

 

 

Vanguard

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending