Connect with us

News

An Bukaci Kotu Ta Dakatar Da Takarar Shugaba Tinubu A 2027, A Bisa Zargin Ya Gabatar Da Shaidar Karatu Na Jabu

Published

on

president bola ahmed tinubu 768x510 (1)
Advertisements
ads

Wata ƙungiya mai rajin samar da  sauye-sauye da wayar da kan al’umma, Centre for Reform and Public Advocacy (CFRPA), ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Kano tana neman a hana Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, bisa zargin gabatar da takardun shaidar karatu da take ikirarin na bogi ne.

A cewar takardun ƙarar da aka gani, ƙungiyar ta yi zargin cewa Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) takardar shaidar karatu daga Chicago State University da kuma takardar shaidar kammala bautar ƙasa (NYSC) da take zargin ba su inganta ba, a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Fulani Sun Ƙauracewa Kasuwar Dabbobi Ta Anchau, Inda Suka Koma Falgore Daji

An shigar da ƙarar mai lamba FHC/K/CS/312/2026, inda aka sanya Shugaba Tinubu, INEC da Chicago State University a matsayin waɗanda ake ƙara.

Masu shigar da ƙarar sun kuma yi iƙirarin cewa Tinubu bai taɓa yin karatu a Government College Lagos kamar yadda aka bayyana ba, suna masu cewa an kafa makarantar ne a shekarar 1974, shekaru huɗu bayan lokacin da ake ikirarin ya kammala karatu.

Haka kuma, ƙungiyar ta ce Shugaban Ƙasar ba ya da ingantacciyar shaidar kammala makarantar sakandare, wadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada a matsayin mafi ƙarancin cancantar neman kujerar shugaban ƙasa.

Advertisement

CFRPA ta ƙara da cewa INEC ba ta ɗauki wani mataki kan takardar ƙorafin da ta aike mata ranar 19 ga Yunin 2026 ba, inda ta nemi a fayyace matsayin cancantar Shugaba Tinubu.

A cikin bayanan ƙarar, ƙungiyar ta kuma yi nuni da hukuncin wata kotu a Amurka da aka yanke a shekarar 2023, wanda ya umarci Chicago State University ta fitar da bayanan karatun Tinubu. Ta yi iƙirarin cewa bayanan sun ƙunshi wasu saɓani da kura-kurai da ke buƙatar bincike.

Daga cikin buƙatun da masu ƙarar suka gabatar akwai umartar INEC ta hana Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, cire sunansa daga jerin ‘yan takara idan ya nemi takara, da kuma ɗaukar wasu matakan shari’a kan takardun da ake zargi.

Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Hukumar INEC da Chicago State University ba su fitar da wata sanarwa ko martani kan zarge-zargen ba. Haka kuma, kotu ba ta yanke hukunci kan ƙarar, don haka zarge-zargen na nan a matsayin waɗanda ake jiran kotu ta yanke hukunci a kansu.

 

 

Advertisement

DAILY TRUST

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending