Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sauya Uniform Din Masu Yi Wa Kasa Hidima NYSC

Published

on

Advertisements
ads

Gwamnatin tarayya ta amince da garambawul ga hukumar masu yi wa kasa hidima (NYSC), a wani mataki na kawo sauyi na farko tun bayan samar da shirin shekaru 53 da suka gabata.

Daga cikin sauye-sauyen da aka amince da su akwai maye gurbin shugabancin soji da na farar hula wajen tafiyar da hukumar, yayin da sojoji za su ci gaba da bayar da tsaro a sansanin.

Sama Da Yan Najeriya 700 Har Yanzu Na Makale A Kasar Afirka Ta Kudu

Haka kuma, gwamnati ta amince da sauya kayan NYSC (Unifirm) domin su dace da sauye sauyen da aka tanadar.

Har ila yau sabon tsarin zai mayar da hankali wajen koyar da sana’o’i da fasahar zamani da jagoranci da ƙwarewar aiki, domin bai wa matasan damar gogewar da za ta taimake su a guraren aiyukansu.

Gwamnatin ta ce an fara wannan aikin na garambawul tun a shekara ta 2025, kuma ana sa ran zai ƙara dacewa da buƙatun ci gaban tattalin arziki da bunƙasa matasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending