News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙarawa Masu Yiwa Ƙasa Hidima NYSC Alawus
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Babban Darakta Janar na Hukumar Kula da masu yiwa ƙasa hidima Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya labarto cewa gwamnatin tarayya na shirin karawa masu NYSC Alawus da zarar an kammala tattaunawar da ake yi kan sabon mafi ƙarancin albashi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa haka kuma shugaban ya gargadi masu yiwa ƙasa hidima da su guji ɗauka hotunan abubuwan da ake yi a sansanin horo suna yaɗawa a soshiyal indiya, dalilin aikata haka an kori wasu ƴan NYSC su uku daga sansanin saboda saba wa wannan doka .
Shugaban ya bayyana hakan ne a yau Asabar yayin da yake jawabi ga mambobin bautar ƙasa su 2762 na Batch B, Stream One, a sansanin NYSC Orientation Camp na jihar Ogun, Sagamu.
Ya bukace su da su dauki horon da ake ba su a sansanin da muhimmanci, duk da cewa horon akwai wahala amma dai su kara kaimi wajen koyo domin su zama ‘yan Najeriya nagari da kuma amfani ga al’umma.
Ahmed ya ce, “Bari kuma in tunatar da ku dokokar da baku sani ba ba a sanya ayyukan sansanin a soshiyal midiya ba, samu abokan aikinku guda uku a wani waje yanzu haka akwai mutum uku da aka kama su da aikata haka ,an more su
