News
Yan Sandan Sun Tabbatar Da Yin Garkuwa Da Wasu ‘Yan Jarida Biyu Da Iyalansu A Kaduna
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, a ranar Lahadi ta tabbatar da yin garkuwa da wasu ‘yan jarida biyu da iyalansu a Kaduna da misalin karfe 10:30 na daren ranar Asabar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mansir Hassan, wanda ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN da faruwar kamarin ya ce jami’ansu na kokarin ganin cewa wadanda abin ya shafa sun samu ‘yanci kuma ba su sumu wani rauni ba a wajan masu garkuwa da mutane ba.
Ya ce: “Mun tura jami’an mu cikin daji inda ana zargin masu garkuwa da mutane ne a yankin.
“Wadanda abin ya rutsa da su su ne shugaban kungiyar ‘yan jarida ta NUJ Council na jihar Kaduna, AbdulGafar Alabelewe da wasu ‘yan uwa guda 3 da aka yi garkuwa da su a daren jiya a Danhono 2, a garin Millennium City, Kaduna.
“Haka zalika, an yi garkuwa da wakilin jaridar Blueprint Abdulraheem Aodo tare da matarsa a wuri guda.
“AbdulGafar Alabelewe kuma shine wakilin jaridar kasa.” (NAN)
