News
RATTAWU Ta Yaba Wa Sunusi Bature Kan Gyaran Motar Ƙungiyar A Kano
Ƙungiyar Ma’aikatan Rediyo, Talabijin, Wasan Kwaikwayo da Fasaha (RATTAWU) reshen Jihar Kano ta nuna jin daɗinta tare da yaba wa Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamnan Kano, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, bisa taimakon da ya bayar wajen gyaran motar ƙungiyar.
Shugaban RATTAWU na Kano, Kwamared Babangida Mamuda Biyamusu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
Yau Shekaru 12 Da Rasuwar Sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero
Ya ce motar ƙungiyar ta daɗe a tsaye sakamakon matsalar na’ura, lamarin da ya haifar da cikas wajen gudanar da wasu ayyukan ƙungiyar da kuma zirga-zirgar mambobinta.
A cewarsa, taimakon da Sunusi Bature ya bayar ya zo a kan lokaci, domin ya taimaka wajen dawo da motar aiki da kuma rage matsalolin sufuri da ƙungiyar ke fuskanta.
“Mun yaba da wannan karamci da aka yi mana. Gyaran motar zai taimaka wajen sauƙaƙa ayyukan ƙungiyarmu da kuma ƙara inganta yadda muke gudanar da al’amuranmu,” in ji Biyamusu.
Ya ƙara da cewa RATTAWU za ta ci gaba da taka rawar gani wajen wayar da kan jama’a da yaɗa bayanai kan manufofi da shirye-shiryen ci gaban da gwamnati ke aiwatarwa.
Shugaban ƙungiyar ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa yadda gwamnatinsa ke aiwatar da shirye-shiryen ci gaba ƙarƙashin manufar Kano First.
Ya bayyana gwamnan a matsayin shugaba mai kusanci da jama’a kuma mai bai wa kafafen yaɗa labarai muhimmanci, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen ƙarfafa yaɗuwar bayanai da ci gaban jihar.
A ƙarshe, RATTAWU ta jaddada kudirinta na ci gaba da inganta ƙwarewa da ƙa’idojin aikin yada labarai tare da goyon bayan duk wani shiri da zai amfanar da al’ummar Kano.
