Connect with us

News

Gaskiya Abin Kunya Ne A Ce Mutum Musulmi Ya Haddace Watannin Miladiya  Amma Bai San Na Musulunci Ba —Malam Khalid Arzai

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

A yayin da a ka shiga sabuwar shekarar musulunci, 1446 H, bincike ya nuna cewa wasu daga cikin al’ummar musulmi musamman matasa ba kasafai su ke rike watannin musulunci ba, ko kuma amfani da shi ba, kamar yadda su ke bibiyar calandar Miladiya.

Al’ummar Musulmi na fara shiga watan Muharram ne a kowace shekarar Musulunci a matsayinsa na watan farko, wanda kuma yake da wasu keɓantattun ayyuka na ibada da tarihi

Wutar Lantarkin Najeriya Ta Dauƙe Gaba Ɗaya A Faɗin Najeriya A Karo Na 4 A 2024

Kasancewarsa wata na farko a kalandar Musulunci, ana kallon watan Muharram a matsayin wata alama ta mafarin sababbin abubuwa a sabuwar shekara.

Fitaccen malamin addini Sheikh Malam Khalid  Arzai ya faɗa wa Jaridar INDA RANKA cewa Muharram ɗaya ne cikin wata huɗu da suka fi alfarma (daraja) a shekarar Musulunci.

Advertisement

“Cikin huɗun ma shi ne [Muharram] ya fi su falala da matsayi kamar yadda ibn Rajab ya ambata,” a cewar Malam Disina.

Ya ƙara da cewa shi ne wata ɗaya cikin watannin shekara guda 12 wanda Allah ya danganta shi zuwa gare shi a cikin Hadisi.

“Manzon Allah SAW ya faɗa da kansa cewa: Shaharullahlil Muharram [Watan Allah mai alfarma].”

Allah ya na cewa “Haqiqa lissafin watanni a wurin Allah guda goma sha biyu ne a cikin littafin Allah tun ranar da Ya halicci sammai da qassai, daga cikin wadannan watanin (12) akwai watanni hudu masu alfarma.[4]

Malaman musulunci sun ce an ambaci watan muharram da suna Muharram ne saboda Allah ya hana yaqi a cikinsa.

Wasu kuma malaman suka ce Allah ya ambaci watan muharram da suna Muharram ne saboda a cikinsa ne Allah ya haramta ma Ibilis (Shaidan) Aljannah.[6]

Advertisement

Zai yi matuqar kyau mu kawo watannin Musulunci guda goma sha biyun da Allah ya ambata a littafinsa mai girma, ga su kamar haka;

1. Muharram.

2. Safar.

3. Rabi’ul Awwal.

4. Rabiut Thani.

5. Jimadal Ula.

Advertisement

6. Jimada Thani.

7. Rajab.

8. Sha’aban.

9. Ramadan.

10. Shawwal.

11. Zulqada.

Advertisement

12. Zulhijja.

Wadannan su ne watannin Musulunci wadanda ya kamata a ce ko wane musulmi ya haddace su, kuma ba za ka same su a cikin Qur’ani ba dole sai ka dawo ma sunnah. wannan shi ne yake qara nuna mana cewa ba za ka taba fahimtar Qur,ani ba sai ka yarda da Hadisi, domin Hadisi shi ne yake fasassara Qur’ani, wanda ya ce ba ruwan sa da Hadisi Qur,ani kawai, to wannan ya bar musulunci, haka Allah ya ce a cikin Qur,ani.[7]

Allah yana cewa “Lalle ne wandanda suke kafirta da Allah da Manzan sa kuma suna so (nufi) su rarrabe tsakanin maganar Allah da maganar Manzon nin sa, kuma suna cewa mun yi Imani da sashin (Qur’ani) kuma muna kafirta da sashe,(Hadisi) ( wato suna cewa sun yarda da Qur’ani ba su yarda da hadisi ba) kuma suna nufi su riqi hanya a tsakanin wannan. Wadannan sune kafirai tsantsa (masu qaryata hadisi suna cewa sun yarda da Qurani kawai) kuma mun yi tattalin azaba mai wulaqantarwa ga kafire.[8]

Wannan aya ta nuna mana cewa duk wanda ya qaryata hadisi ya bar musulunci.Nemi fassaran ta wajen malamai. Maganar wata ya zo cikin Qur,ani amma bayanin su filla-filla ya zo cikin Hadisi ne”.[9]

Gaskiya abin kunya ne a ce mutum musulmi ya haddace watannin kafirci tun daga January zuwa December amma bai san na Musulunci ba, wanda asalin watannin kafirci guda biyar ne, daga baya suka kwaikwayi na musulunci suka maida nasu zuwa goma sha biyu. Kuma dukkanin watannin kafirci sunaye ne na gumakan qasar Girka [Greak].[10] Lalle ya kamata yara su tabbatar sun haddace watannin musulunci.

Zamanin Manzon Allah (SAW) babu cewa an shiga sabuwar shekara. An fara qirgar sabuwar shekara ne zamanin Khalifa Umar Dan Khaddabi Allah ya qara masa yarda, shi ne ya tsara hijra har aka sami tarihin hijira ta musulunci. Idan an fahinci wannan za’a fahinci cewa duk wata magana da ta zo a kan yin wata sallah ko wata addu’a a sabuwar shekara.

Advertisement

Kamar yadda aka san wasu watannin Musulunci sun keɓanta da wasu ibadu, haka shi ma Muharram na da nasa abubuwan da ake buƙatar Musulmai su dinga yi.

Malam Khalid a bayyana wasu na’ukan azumi a matsayin babbar ibadar da ake son a dinga yi. Su ne:

Yawaita azumi domin Annabi SAW ya ce: “Mafificin Azumi bayan azumin watan Ramadan shi ne azumi a watan Al-Muharram”, Muslim ya rawaito.

Yin azumin ranar 10 ga watan Muharram (azumin Ashura) domin Annabi SAW ya ce: “Azumin Ashura yana kankare zunuban shekarar da ta gabata”, Muslim ya rawaito.

Musulunci ya hana fara yaƙi a cikinsa ko kaima wasu farmaki.

Dan haka zai yi kyau duk musulmi ya runga amfani da lissafin watannin muslunci Saboda ta haka ne mutum zai runga bibiyar abubuwan da ke Maimaituwa a addinin muslunci na ibada kamar Azumi, Babbar Sallah, Karamar Sallah, shigar sabuwar Shekara , fitar Shekara , Hajji , Maulud , da dai sauran su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending