News
Wutar Lantarkin Najeriya Ta Dauƙe Gaba Ɗaya A Faɗin Najeriya A Karo Na 4 A 2024
DAGA YAASIR SANI ABDULLAHI
Wutar lantarki ta dauƙe gaba ɗaya a faɗin Najeriya sakamakon durƙushewar babban layin lantarkin ƙasar.
Wutar lantarkin ta sake ɗaukewa gaba ɗaya ne, bayan da ta ragu zuwa 0.80 a ranar Asabar.
Kasashen Africa Nijar, Mali, da Burkina Ba Za su dawo Kan tsarin Kungiyar ECOWAS ba – Janar Tiani
Binciken da aka yi a shafin intanet na kamfanin da ke kula da wutar lantarkin ya nuna yadda ya fara raguwa da misalin ƙarfe 2 na rana zuwa megawat 2,797.16.
Ƙarfin wutar lantarki ya ƙara raguwa zuwa 1,020.08 da misalin ƙarfe 3 na rana kafin ya ƙasa sosai zuwa 0.80 da misalin ƙarfe 4 na yamma.
Rahotanni na nuni da cewa ta ruwaito cewa 0.80 shi adadin abin da babban layin samar da wutar lantarki ke da shi a yanzu haka.
Wannan shi ne karo na huɗu da babbar tashar samar da wutar lantarki ta Najeriya ke faɗuwa a 2024.
