News
Kasashen Africa Nijar, Mali, da Burkina Ba Za su dawo Kan tsarin Kungiyar ECOWAS ba – Janar Tiani
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Shugaban Mulkin Sojan Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tiani a ranar Asabar ya ce ƙasarsa tare da makwabtansu da suka hadar da Mali, da Burkina Faso sun juya baya ga kungiyar kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS.
Shugaban ya bayyana hakan ne a Niamey a yayin buɗe taron da aka shirya tsakanin ƙasashen uku da suka fice daga cikin babbar kungiyar a farkon wannan shekarar.
“Ƙasarmu tana nan akan bakanta na juya baya ga Kungiyar raya Kasashen Afirka ta ECOWAS “in ji Tiani.
Shugaban kungiyar ta ECOWAS Dr. Omar Alieu Touray a ranar Alhamis ya koka da cewa duk da kokarin da kungiyar ke yi na dawo da kasar Mali, da Burkina Faso, da Nijar amma kasashen uku ba su nuna alamun dawowar su ba.
A yayin da yake jawabi a wajen bude taro karo na 92 na Majalisar Ministocin Kungiyar a Abuja, ya ce har yanzu kungiyar ECOWAS ba ta bi wata hanya mai tasiri ba wajen tattaunawa da mahukuntan kasashen Sahel ukun kan matakin da suka dauka na janyewar su daga kungiyar ba.
A ranar 28 ga watan Junairun da ya gabata ne dai kasashen Burkina Faso, da Mali da Nijar suka sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS.
Duk da matakan sasanci da muka yi ta bi, da kuma hanyar sassauta takunkumi, gami da gayyatar Gwamnatocin zuwa zaman tattaunawa, amma har yanzu ba mu samu wata alamr da ke nuna yiyuwar dawowar kasashen ba, “in ji Touray.
Taron da aka yi a ranar Asabar a Niamey babban birnin Jamhuriyar Nijar ya kasance karo na farko tsakanin Shugabannin Mulkin Sojojin sabuwar kungiyar kawancen kasashen yankin Sahel (AES).
Mali, da Burkina Faso, da Nijar sun kulla yarjejeniyar kare muradun juna bayan fitar su daga kungiyar ta ECOWAS a watan Janairu.
