Connect with us

News

Gwamnatin Kano Za Ta Ƙaddamar da Shirin Haɗa Gwiwa Da Ƙungiyoyin Fararen Hula Domin Haɓaka Ci Gaban Jihar – Bilkisu Indabo

Published

on

20260802 081845 COLLAGE

Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kano Shawara ta Musamman kan Harkokin Wayar da Kai, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ta bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin ƙaddamar da wani tsari na haɗin gwiwa da ƙungiyoyin fararen hula domin ƙara inganta aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da kuma kusantar da su ga al’umma.

Shirin mai suna Government–NGO Handshake na da nufin samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin fararen hula, domin ƙarfafa wayar da kan jama’a, inganta gaskiya da riƙon amana, tare da bai wa al’umma damar shiga cikin shirye-shiryen raya jihar.

Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku

A cewar Bilkisu Indabo, ƙungiyoyin fararen hula za su tallafa wa gwamnati ta hanyar wayar da kan jama’a, bayar da shawarwari, tattara ra’ayoyin al’umma da kuma tabbatar da cewa manufofi da ayyukan gwamnati sun isa ga kowane rukuni na al’umma, musamman mata, matasa, masu buƙata ta musamman da sauran masu rauni.

Ta ce shirin zai kuma ƙarfafa sadarwa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin fararen hula, tare da samar da tsarin karɓar ra’ayoyi da ƙorafe-ƙorafen jama’a domin inganta aiwatar da manufofi da ayyukan raya ƙasa.

Bilkisu Indabo ta ƙara da cewa haɗin gwiwar zai bai wa jama’a damar shiga cikin tsarawa, aiwatarwa da kuma sanya ido kan ayyukan ci gaba, lamarin da zai ƙara inganta gaskiya, riƙon amana da tasirin ayyukan gwamnati.

Advertisement

Ta bayyana cewa za a sanar da ranar ƙaddamar da shirin nan ba da jimawa ba, inda ake sa ran zai zama wani muhimmin mataki na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin fararen hula domin cimma ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kano.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending