News
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Grow Homes Estate, Sun Yi Garkuwa Da Mutane Biyu
Wasu ƴan bindiga dauke da muggan makamai sun kai wani mummunan hari a unguwar Grow Homes Estate da ke Chikakore, kusa da Kubwa a birnin tarayya Abuja, inda suka sace wani ɗan kasuwa da wata mata a safiyar Litinin, 26 ga watan Mayu, 2025.
Bayanan da wakilinmu ya tattara sun nuna cewa maharan sun kutsa cikin unguwar ne da misalin ƙarfe 3 na dare, inda suka kai farmaki gida uku, suka fasa tagogi tare da tilasta shiga gidajen, sannan suka yi awon gaba da mutane biyu.
Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Wike Kan Kwace Filaye 4,794 a Abuja, Ya Ba da Wa’adi
Wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Leadership Hausa cewa “sun sare wayar lantarki da ke kan katanga, suka fasa taga suka shiga gida. Ba mu da wani tsaro da ya dace a nan.”
Bayan kai harin, rahotanni sun bayyana cewa maharan sun saki matar da suka yi garkuwa da ita, yayin da suka ci gaba da tafiya da ɗan kasuwar cikin daji.
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’anta sun yi musayar wuta da maharan na tsawon mintuna 40, lamarin da ya kai ga kubutar da matar.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike tare da kokarin ganin an ceto ɗan kasuwan da ke hannun masu garkuwar.
“Mun tura jami’anmu cikin gaggawa bayan samun kiran gaggawa daga mazauna unguwar, kuma mun yi nasarar ceto daya daga cikin wadanda aka sace. A halin yanzu, jami’anmu na cikin dajin suna ci gaba da bin sawun maharan domin ceto wanda ya rage,” in ji SP Adeh.
Wannan lamari dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan wani makamancin hari da aka kai a Efab Estate da ke Idu, abin da ke kara tayar da hankalin mazauna Abuja, musamman yankunan da ke kan iyakar birnin.
Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne karo na uku da ake kai irin wannan hari a wannan yanki cikin ‘yan watannin nan, abin da ke kara jaddada bukatar sake duba tsarin tsaro a manyan unguwannin birnin.
