News
Yan Bindiga Sun Sace Uwa Mai Shayarwa Da Yara 6 A Edo
’Yan bindiga sun sace yara da wasu ’yan uwa a jihar Edo, a wani hari da ya faru a yankin Evboneka da ke kan hanyar Benin zuwa Akure.
Lamarin ya faru da misalin karfe biyar na yammacin Litinin, 2 ga Fabrairu, 2026, yayin da mutanen ke dawowa daga makaranta.
Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudurin Gyaran Dokar Zaɓe Bayan Tattaunawa Mai Tsawo
An ce daga cikin wadanda aka sace akwai wata uwa mai shayarwa da ’ya’yanta, sai dai an sake ta tare da jaririnta.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun ceto wasu yara uku, amma har yanzu mutane hudu na hannun masu garkuwa da su.
Iyalan sun ce masu garkuwar sun tuntube su tare da bukatar Kuɗin fansa Naira miliyan 260.
Rundunar ’yan sandan jihar Edo ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ana ci gaba da kokarin cafke masu laifin da ceto sauran mutanen da ke hannunsu.
-
News4 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News1 day ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News9 hours ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
