News
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohon Shugaban APC A Kebbi

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Koko/Besse da ke Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Besse, ya rasu a hannun ’yan bindiga bayan shafe makonni yana tsare a hannunsu sakamakon sace shi da aka yi a farkon watan Yunin 2026.
Marigayin ya shiga hannun masu garkuwa da mutanen ne tare da wani abokinsa, Malam Muhammadu Maibarga, fitaccen malamin addini na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), wanda shi ma ya rasu tun da farko yayin da yake tsare a hannun masu garkuwar.
Kudirin Kafa Yansandan Jahohi Na Iya Lashe Sama Da Naira Biliyan 800 —Masana
Kafin rasuwarsu, wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna mutanen biyu cikin wani daji, inda masu garkuwar suka rika wulaƙanta su, lamarin da ya tayar da hankalin jama’a tare da ƙara nuna tsananin matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce rundunar na ci gaba da bincike kan rahoton rasuwar tsohon shugaban jam’iyyar, tare da ɗaukar matakan gano waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban shari’a.
Wannan lamari ya sake jaddada ƙalubalen rashin tsaro da ke addabar wasu sassan Arewacin Najeriya, inda hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane ke ci gaba da haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
