News
Jami’an Yansanda Sun Kama Matashi Kan Zargin Kashe Dan Uwansa Da Matarsa A Kebbi
Rundunar Ƴansandan Najeriya reshen Jihar Kebbi ta kama wani matashi mai suna Idrisu Musa bisa zargin kashe babban ɗan uwansa, Muhammed Haruna, da matarsa Habiba Muhammed a ƙaramar hukumar Jega.
Punch ta rawaito cewa, kakakin rundunar Ƴansandan jihar, Bashir Usman, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:15 na safiyar ranar 9 ga Mayu a ƙauyen Asarara da ke gundumar Kimba, inda aka kai wa ma’auratan hari da adda yayin da suke barci.
Ciyawa Mai Guba Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Shanu 80 A Adamawa
Sanarwar ta ce ma’auratan sun mutu ne sakamakon munanan raunukan da suka samu, yayin da binciken farko ya nuna wanda ake zargin ya taɓa yi musu barazana a baya.
Kakakin rundunar ya ce an samu wasu hujjoji da ke alaƙanta wanda ake zargin da aikata laifin.
Ya ƙara da cewa kwamishinan Ƴansandan jihar, Umar M. Hadejia, ya bayar da umarnin miƙa batun zuwa sashen binciken manyan laifuka domin zurfafa bincike.
