News
Ƴan Ta’adda Sun Kashe Mutum 6 Tare Da Yin Garkuwa Da Sama Da 100 A Kebbi
Ƴan ta’adda sun kai hari a wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Danko Wasagu da ke jihar Kebbi, inda suka kashe aƙalla mutane shida tare da yin garkuwa da fiye da mutane 100.
Harin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a kauyukan Ali da Dan Mutari, wadanda ke kusa da kauyen Mai Rairai a cikin mazabar Bena.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa mahara sun shigo ne daga gefen da ke iyaka da kananan hukumomin Anka da Bukkuyum na jihar Zamfara, inda suka dade suna gudanar da irin waɗannan hare-hare.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a ɓoye sunansa saboda tsaro, ya ce: “Mun san akwai jami’an tsaro a kauyen Mai Rairai, amma ba su da isassun kayan aiki ko ababen hawa da za su iya tinkarar waɗannan mahara.”
Yankin iyaka tsakanin Kebbi da Zamfara da kuma hanyar da ke zuwa jihar Neja na ci gaba da zama cibiyar da ƴan ta’adda ke fakewa domin kai farmaki a sassa daban-daban na Arewa maso Yamma.
Sai dai har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da sanarwar hukuma kan lamarin ba, kuma ana ci gaba da bibiyar halin da al’ummar da abin ya shafa ke ciki.
