News
Kano: ’Yan Sanda Sun Kama Mutane 41 Kan Kisan DPO A Rano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan gilla da aka yi wa Baturen ’Yan Sanda na Rano (DPO), CSP Baba Ali, yayin da yake bakin aiki.
Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ta kammala wani bincike mai zurfi da ta gudanar kan lamarin, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma da kuma fargaba a zukatan mazauna yankin.
AMBALIYAR RUWA: Mutum 21 Sun Rasa Rayukansu, Gidaje 50 Sun Lalace A Neja
A wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan Sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a madadin Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, rundunar ta bayyana cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin wadanda suka aikata wannan ta’asa sun fuskanci hukunci.
“An kama mutane 41, ciki har da wadanda muka samu da kwararan hujjoji na hannu a lamarin. Runduna ba za ta sassauta ba sai gaskiya ta tabbata,” in ji SP Kiyawa.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa babu wanda zai aikata laifi ya tsira da shi.
“Duk wanda ke da hannu a wannan mummunan aiki, lallai zai fuskanci hukunci,” in ji shi.
