News
“Sai Kana Raye Za Ka Iya Ba Da Rahoton Abin Da ke Faruwa ” — Abbas Ibrahim Ya Gargaɗi ‘Yan Jarida
Amintaccen Memba na Shiyya ta A na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Kwamared Abbas Ibrahim, ya buƙaci ‘yan jarida da su fifita kare rayukansu yayin gudanar da rahotannin zaɓe, yana mai cewa babu wani labari da ya kai darajar rayuwar ɗan jarida.
Abbas Ibrahim ya bayyana hakan ne a Kano yayin gabatar da takarda mai taken “Ethical, Responsible and Safe Election Reporting: Building Towards the 2027 Elections” a taron horas da ‘yan jarida da Kano Online Media Chapel ta shirya domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
Ya ce lokutan zaɓe na kasancewa cikin mafi haɗarin lokuta ga masu aikin jarida, saboda yawaitar tashin hankali, barazana, tsangwama da hare-hare kan masu aikin yaɗa labarai.
A cewarsa, saboda haka ya zama wajibi ga ‘yan jarida su yi cikakken nazarin haɗarin da ke tattare da wurin da za su je kafin fita aiki, su sanar da editocinsu inda za su kasance, tare da kasancewa da katin shaidar aiki da hanyoyin sadarwa na gaggawa.
Abbas Ibrahim ya jaddada cewa ɗa’ar aikin jarida ita ce ginshiƙin sahihin rahoton zaɓe. Ya ce rahotanni su kasance bisa gaskiya, adalci, rashin son kai da tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa.
Ya kuma yi gargaɗi game da yaɗuwar labaran ƙarya da bayanan yaudara a kafafen sada zumunta, yana mai cewa bai kamata ɗan jarida ya wallafa hoto, bidiyo ko wani saƙo ba tare da tabbatar da sahihancinsa daga majiyoyi masu inganci ba.
Dangane da rahoton rikice-rikicen zaɓe, Abbas Ibrahim ya ce ya kamata kafafen yaɗa labarai su guji kalaman da za su iya rura wutar rikici ko ƙara rarrabuwar kawuna, tare da bai wa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa damar bayyana matsayinsu.
Ya kuma buƙaci ‘yan jarida su guji shiga tsakiyar tarzoma ko gardama da jami’an tsaro ko magoya bayan jam’iyyun siyasa, yana mai cewa kare rayuwa shi ne mataki na farko kafin gudanar da aikin jarida.
“Ka kasance a raye domin ba da rahoto, ba kai ne labari ba. Idan ba ka kula da tsaron kanka ba, kai ne za ka zama abin da ake ba da rahoto,” in ji Abbas Ibrahim.
Ya kuma yi kira ga gidajen yaɗa labarai su ƙara saka hannun jari wajen horas da ma’aikatansu kan tsaro, tabbatar da hanyoyin tantance bayanai da kuma samar da tsare-tsaren gaggawa ga masu aikin rahoton zaɓe.
A ƙarshe, ya ce yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, akwai buƙatar ‘yan jarida su haɗa ƙwarewa da bin ƙa’idojin aikin jarida da kuma kiyaye lafiyarsu, domin a cewarsa, sahihan bayanai da sahihin zaɓe suna tafiya tare da tsaron ɗan jarida.
