Connect with us

News

Bai Kamata ‘Yan Najeriya Su Ci Gaba Da Yin Girki Da Itace Ba — Minista

Published

on

images

Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur mai kula da harkokin Iskar Gas, Ekperikpe Ekpo, ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su ci gaba da amfani da itace wajen girki ba, alhali ƙasar na da yalwar iskar gas.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da shirin Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa amfani da iskar gas domin girki, wanda aka gudanar a birnin Yenagoa na Jihar Bayelsa.

“Sai Kana Raye Za Ka Iya Ba Da Rahoton Abin Da ke Faruwa ” — Abbas Ibrahim Ya Gargaɗi ‘Yan Jarida

Ya ce manufar shirin ita ce tabbatar da cewa gidaje a faɗin ƙasar sun samu damar amfani da makamashi mai tsafta, wanda zai taimaka wajen kare lafiyar al’umma da kuma rage sare bishiyoyi.

 

A cewarsa, bai kamata uwa ta kasance cikin yanayin zaɓar tsakanin ciyar da iyalanta da kuma kare lafiyarsu ba, yana mai cewa hayaƙin da ke fitowa daga amfani da itace wajen girki na haddasa matsalolin lafiya, musamman ga mata da yara.

Advertisement

Ekpo ya kuma ce bai dace mutane su ci gaba da ɓata lokaci suna neman itacen girki ba, alhali Allah Ya albarkaci Najeriya da dimbin iskar gas da za a iya amfani da ita a matsayin makamashi mai tsafta.

Ya bayyana cewa shirin zai gudana ne cikin haɗin gwiwa da kamfanonin makamashi da suka haɗa da Seplat Energy, ExxonMobil, NNPC, NLNG, Dangote Group, SPDC da TotalEnergies domin tabbatar da isar da iskar gas ga al’umma.

Ministan ya ce Najeriya na da sama da tiriliyan 215 cubic feet na iskar gas da aka tabbatar tana da shi, lamarin da ya sanya ta cikin ƙasashen da suka fi arzikin wannan albarkatu a duniya.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu> ta himmatu wajen bunƙasa amfani da iskar gas domin samar da makamashi mai tsafta, inganta lafiyar al’umma da kuma ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending