Connect with us

News

ZAƁEN 2027: CHRICED ta ƙarfafa ’yan jarida, CSOs kan kare haƙƙin jama’a

Published

on

IMG 20260910 160914 827

Cibiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam da Ilimantar da Jama’a (CHRICED) ta shirya taron kwana biyu da ya haɗa ’yan jarida da wakilan ƙungiyoyin fararen hula (CSOs), domin ƙarfafa musu ƙwarewa wajen inganta zaɓe da kare haƙƙin jama’a a Najeriya.

Taron wanda aka gudanar domin ƙarfafa rawar da kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin fararen hula ke takawa a harkokin dimokuraɗiyya, ya mayar da hankali kan wayar da kan masu zaɓe, tantance sahihancin bayanai, sa ido kan zaɓe da kuma kare haƙƙin jama’a.

Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu

Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Kamilu Sani Fage na Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin fararen hula na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sahihin zaɓe.

Ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen wayar da kan masu zaɓe, yaƙi da yaɗuwar bayanan ƙarya, sa ido kan harkokin zaɓe da kuma samar da sahihan rahotanni ga jama’a. Ya ƙara da cewa ya kamata a gudanar da zaɓe bisa gaskiya, adalci, ’yanci da kuma bayyana gaskiya.

Shi ma Farfesa A.B. Ahmed na Sashen Shari’a na Jami’ar Bayero, ya ce sahihin zaɓe dole ne ya kasance bisa doka da adalci, tare da bai wa kowane ɗan ƙasa damar shiga harkokin siyasa da kuma zaɓar shugabannin da yake so.

Advertisement

Ya ce tabbatar da ’yancin jama’a da kuma gaskiya a tsarin ƙidaya da bayyana sakamakon ƙuri’u na daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin zaɓe.

A nata jawabin, Sakatariyar NUJ Reshen Jihar Kano, Hauwa Zaradeen, wadda ta wakilci Shugaban ƙungiyar, Kwamared Sulaiman Dederi, ta buƙaci a ci gaba da shirya irin waɗannan tarukan horaswa ga ’yan jarida da ƙungiyoyin fararen hula.

Ta ce horaswar za ta taimaka wajen ƙara wa ’yan jarida da masu fafutukar kare haƙƙin jama’a ilimi da ƙwarewa, musamman wajen tunkarar sabbin barazanar da ke fuskantar ’yancin jama’a da aikin jarida a lokacin zaɓe.

Mahalarta taron sun kuma jaddada aniyarsu ta ci gaba da kare ƙa’idojin dimokuraɗiyya, haƙƙin jama’a da kuma tallafa wa tsarin zaɓe mai gaskiya, adalci da sahihanci a Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending