News
An hallaka wani dalibin Jami’ar Jos har lahira bisa zargin satar waya
Wani ɗalibin Jami’ar Jos mai suna Ibrahim Mbaya ɗan shekaru 25 ya rasa ransa, sakamakon dukansa da ake zargin ɗalibai sun yi bisa zargin satar wayar hannu.
lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a ɓangaren kwanan ɗaliban da ke wajen makarantar, kusa da yankin City of David a kan titin Ring Road a birnin Jos ɗin jihar Plateau.
Hatsarin Mota Ya Janyo Cunkoso A Ƙarƙashin Gadar Shataletalen Dangi A Kano
Wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda waɗanda ake zargin su ka yi ta dukan matashin, tare da yi masa uƙuba iri-iri da hakan ya yi sanadiyyar rasa ransa.
Wata majiya ta shaida cewa ɗalibin Ibrahim Mbaya ya halarci wani taron shagali ne a jami’ar inda daga bisani ya yanke shawarar kwana a gidan abokinsa da ke Ring Road, saboda dare ya yi sosai kafin ya koma gidansa da ke Rayfield.
Majiyar ta ƙara da cewa bayan gari ya waye ne abokansa su ka bayyana cewa sun rasa wayar hannu ƙirar iPhone kuma tunda su kaɗai ne a cikin ɗakin to dole shi ne ya ɗauka, daga nan su ka fara dukansa har ya rasa ransa.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Plateau ta tabbatar da kama mutane uku da ake zargi da hallaka matashin.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Alabo Alfred, ya yi Allah wadai da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa waɗanda ake zargin su na tsare a hannunsu yanzu haka domin faɗaɗa bincike.
Rundunar ƴan sanda ta kuma gargaɗi mazauna yankin da su gujewa ɗaukar doka a hannu, sakamakon an tanadi dokoki domin yin bincike da gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifuka, kuma duk wanda ake zargi yana da ƴancin wannan damar.
