News
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Makarantu A Kananan Hukumomi 20
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare da ke ƙananan hukumomi 20 cikin 23 na jihar, sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro da ake fuskanta a wasu sassan jihar.
Wata takarda da aka aika wa shugabannin makarantu ta umarci dukkan makarantun da abin ya shafa da su dakatar da karatu daga ranar Litinin har sai gwamnatin jihar ta bayar da wani sabon umarni.
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Makarantu A Kananan Hukumomi 20
Sai dai umarnin bai shafi makarantun da ke ƙananan hukumomin Sakkwato ta Arewa da Sakkwato ta Kudu ba. Haka kuma, wasu tsirarun makarantu da ke ƙananan hukumomin Wamakko da Dange Shuni ba sa cikin waɗanda aka umarci su rufe.
Wani malami da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa an sanar da su rufe makarantar da yake koyarwa. Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan ƙaruwa da hare-haren ‘yan bindiga a yankunan gabashi da kudancin jihar.
A cewarsa, hare-haren da ake kai wa garuruwa da ƙauyuka sun ƙaru a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya sa gwamnati ta ɗauki wannan mataki domin kare rayuka da lafiyar ɗalibai, malamai da sauran ma’aikatan makarantu.
Ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin jihar bai yi nasara ba, domin wasu jami’an gwamnati sun ce an umarce su da kada su yi magana kan lamarin, kasancewar takardar umarnin ta kasance ta cikin gida.
Sai dai wani jami’in gwamnati da ya buƙaci a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa an ɗauki matakin ne saboda dalilan tsaro, domin tabbatar da kare lafiyar ɗalibai da malamai yayin da ake ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren ‘yan bindiga a wasu sassan jihar.
Ana sa ran gwamnatin jihar za ta ci gaba da sa ido kan halin tsaro kafin yanke hukuncin lokacin da makarantun za su koma gudanar da karatu.
