Connect with us

News

Budurwa Ta Yanke Mazakutar Saurayinta Yayin Da Yake Barci A Kano

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wata matashiya mai shekaru 25 da ake zargi da yanke mazakutar saurayinta a wani otal da ke unguwar Badawa a Kano.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Litinin, bayan da suka samu rahoton abin da ya faru.

Ana Fargabar Dalibai Sun Maƙale Bayan Rushewar Ginin Dakunan Kwana Mai Ɗakuna 90 A Anambra

Ya bayyana cewa mutumin da abin ya shafa da kuma wadda ake zargin duk ’yan asalin Jihar Jigawa ne, amma lamarin ya auku ne a Kano.

A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa matar ta zo daga Maigatari da wata wuka, wadda ake zargin ta yi amfani da ita wajen aikata laifin.

Kiyawa ya ce wadda ake zargin ta shaida wa jami’an tsaro cewa ta aikata hakan ne lokacin da saurayin nata ke cikin barci bayan ya sha maganin ciwon kai.

Advertisement

Ya ƙara da cewa bayan faruwar lamarin, matar ta yi ƙoƙarin kai saurayin zuwa banɗaki domin tsaftace jinin da ya zuba kafin mutanen da ke kusa suka gano abin da ya faru tare da sanar da jami’an tsaro.

Dangane da jita-jitar cewa an yi amfani da wani sinadari ko kayan maye kafin aukuwar lamarin, kakakin rundunar ya ce har yanzu babu wata hujja da ke tabbatar da hakan.

Ya ce jami’an ’yan sanda sun samu kwalbar abin sha da ruwa a cikin ɗakin otal ɗin, kuma ana ci gaba da bincike domin gano ko suna da alaƙa da abin da ya faru.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa saurayin yana raye kuma yana samun kulawar likitoci a wani asibiti.

A halin yanzu, wadda ake zargin tana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da ita a gaban kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending