Connect with us

News

Masana Kiwon Lafiya Sun Nuna Damuwa Kan Karuwar Mutuwar Mata Masu Juna Biyu

Published

on

juna biyu

Masana kiwon lafiya a Jihar Ogun sun yi gargadi kan karuwar mutuwar mata masu juna biyu, inda suka danganta lamarin da yawaitar zubar da ciki ba bisa ka’ida ba da kuma dogaro da masu aikin lafiya marasa kwarewa maimakon kwararrun likitoci.

Masanan sun bayyana hakan ne a wani taron horaswa na kwana guda da aka shirya wa kungiyoyin fararen hula kan  haihuwa da dabarun rage zubar da ciki , wanda aka gudanar a Abeokuta, babban birnin jihar.

Advertisement

Khamenei Ya Yi Gargaɗi Kan Yaƙin Yanki Idan Amurka Ta Kai Hari Kan Iran

Da take jawabi a taron, shugabar Kungiyar Likitocin Mata ta Najeriya (MWAN) reshen Jihar Ogun, Dr Deborah Osisanwo, ta ce kare rayuwar uwa ya zama wajibi, tana mai jaddada bukatar gujewa ayyukan mutanen da ba su da horo ko izini a fannin lafiya.

Advertisement

A cewarta, yawaitar zubar da ciki ba bisa ka’ida ba na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa mace-macen mata masu juna biyu, lamarin da ke bukatar daukar matakan gaggawa daga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

“Bai dace mutanen da ba su da horo ko izini a fannin lafiya su rika tsoma baki a batutuwan zubar da ciki ba. Dole ne a rika tura marasa lafiya zuwa manyan asibitoci domin ceto rayukansu,” in ji ta.

Advertisement

Masana sun kuma bukaci shugabannin al’umma, kungiyoyin fararen hula da hukumomin gwamnati da su hada kai wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin kula da lafiyar mata masu juna biyu, musamman a yankunan karkara.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY REPORTS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending