Connect with us

News

Kwana 8 Kacal Shugaba Tinubu Ya Yi A Najeriya A 2026 — Peter Obi

Published

on

Peter Obi, ya soki Shugaba Bola Tinubu, bisa lokacin da ya shafe a ƙasashen waje a watan Janairun 2026, maimakon mayar da hankali wajen ciyar da ƙasarsa gaba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce ya kamata shugabanni su fi mayar da hankali kan matsalolin cikin gida maimakon tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.

Advertisement

“Yayin da shugabannin wasu ƙasashe ke mayar da hankali kan shugabanci a cikin gida a watan Janairu, shugaban Najeriya ya fifita tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje sama da matsalolin da ke damun al’umma,” in ji Obi.

Obi, ya ce Najeriya na fama da manyan matsaloli kamar rashin tsaro, sace-sace, ƙarancin abinci, rufe makarantu, yajin aikin ma’aikata da kuma ƙarancin wutar lantarki.

Advertisement

“Rashin tsaro ya ƙaru matuƙa a faɗin ƙasar nan. Manoma ba sa iya zuwa gonakinsu, kuma ƙarancin abinci na ƙara tsananta,” a cewarsa.

Ya kuma soki jam’iyyar APC mai mulki, inda ya zarge ta da mayar da hankali kan harkokin siyasa sama da kula da halin da ’yan Najeriya ke ciki.

Advertisement

“Jam’iyyar APC ta fi damuwa da gangami da karɓar masu sauya sheƙa sama da magance matsalolin da al’ummar Najeriya ke fuskanta,” in ji Obi.

Obi, ya kuma tambayi dalilin da ya sa Tinubu ya kwashe kwanaki 23 a ƙasashen waje a watan Janairu, yana cewa ya kamata shugaban ya zauna a gida domin tunkarar matsalolin ƙasar.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending