Connect with us

News

‎Dr. Aminu Magashi Ya Kai Tallafin Gaggawa Bayan Ruwan Sama Ya Lalata Gidan Gyaran Hali Na Mata A Bichi

Published

on

IMG 20260728 173239 663

‎Dr. Aminu Magashi Garba, tare da jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), sun kai ziyarar jaje tare da kai tallafin gaggawa zuwa Gidan Gyaran Hali na Mata da ke Bichi bayan mummunar iska da ruwan sama da suka yi barna a cibiyar.

‎A yayin ziyarar, Dr. Magashi ya raba kayan tallafi da suka haɗa da barguna, magunguna da kayan abinci ga matan da ke zaune a cibiyar domin rage musu radadin ibtila’in da ya afku.

“Kada Wani Ɗan Siyasa Ya Zo Wajena Yana Neman A Saki Ɗan Daba Idan Muka Kama Shi ” — Rimin-Gado

‎Ya kuma zagaya domin duba irin barnar da iska ta haddasa, inda ta kwashe rufin wasu gine-ginen cibiyar tare da rushe wasu sassan katangar harabar gidan.

‎Dr. Magashi ya yabawa Hukumar SEMA kan matakin gaggawar da ta ɗauka na mayar da matan zuwa Gidan Gyaran Hali na Maza da ke Bichi domin tabbatar da tsaron lafiyarsu har zuwa lokacin da za a kammala gyaran cibiyar.

‎Ya ce zai haɗa kai da Gwamnatin Jihar Kano, ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran abokan hulɗa domin samar da ƙarin tallafi ga Hukumar SEMA wajen inganta kula da cibiyoyin gyaran hali guda 13 da ke ƙarƙashinta.

Advertisement

‎A cewarsa, tun kafin wannan ibtila’i ya kai ziyara cibiyoyi shida daga cikin cibiyoyin gyaran hali 13 na jihar, inda ya ba su tallafin magunguna, kayan abinci da sauran kayan masarufi, tare da shirya horo na musamman ga ma’aikatan lafiya da ke aiki a cibiyoyin domin inganta ayyukan kula da lafiyar waɗanda ke cikinsu.

‎Dr. Magashi ya jaddada cewa zai ci gaba da bayar da gudunmawa wajen tallafa wa marasa galihu da cibiyoyin kula da jama’a domin inganta walwala da kare rayuwar al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending