News
Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Dakatar Da Hukuncin Soke Rajistar ADC Da Wasu Jam’iyyu
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke, wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyun siyasa huɗu.
Kotun ta bayar da umarnin ne bayan jam’iyyun da abin ya shafa sun shigar da ƙarar ɗaukaka ƙara, inda suka nemi a dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an kammala sauraron shari’ar.
A hukuncin da ta yanke, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta umurci INEC da kada ta ɗauki wani mataki na soke rajistar jam’iyyun har sai an kammala sauraron ƙarar da ke gabanta.
Tun da farko, Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya ya umarci INEC ta soke rajistar jam’iyyar ADC da Accord Party tare da wasu jam’iyyu uku, bisa zargin rashin cika wasu sharuɗɗan da kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe suka tanada.
Sai dai kwamitin alƙalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara ya bayyana cewa akwai buƙatar a fara sauraron ƙorafin masu ƙara kafin a aiwatar da hukuncin kotun ƙasa, yana mai jaddada muhimmancin kare haƙƙin dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.
Matakin da kotun ta ɗauka na nufin jam’iyyun za su ci gaba da kasancewa a matsayin sahihan jam’iyyun siyasa har zuwa lokacin da za a yanke hukunci na ƙarshe kan shari’ar.
