News
Atiku Ya Zargi Gwamnatin Shugaba Tinubu Da Ɓoye Naira Tiriliyan 8.8 Don Tunkarar Zaɓen 2027
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma jagoran jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɓoye kusan Naira tiriliyan 8.8 daga cikin kasafin kuɗin ƙasa, yana mai cewa ana iya amfani da kuɗin wajen shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan rahoton Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF), wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa a ranar 1 ga Yulin 2026. Rahoton ya ce gwamnatin Najeriya ba ta bayyana wasu kuɗaɗen gwamnati da suka kai kusan kashi biyu cikin ɗari na tattalin arzikin ƙasar (GDP) a cikin kasafin kuɗin baya-bayan nan ba.
Yadda Hayaƙin Janareta Ya Hallaka Saurayi Da Budurwa A Kuros Riba
A cewarsa, idan aka yi la’akari da girman tattalin arzikin Najeriya da ya kai kusan Naira tiriliyan 441.5, hakan na nufin an kashe kusan Naira tiriliyan 8.8 ba tare da an bayyana su a cikin takardun kasafin kuɗi ba, lamarin da ya ce ya hana ’yan Najeriya sanin yadda aka kashe waɗannan kuɗaɗe.
Atiku ya bayyana wannan zargi a matsayin ɗaya daga cikin batutuwan da suka fi tayar da hankali a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya, tare da yin kira ga ’yan Najeriya, kafafen yaɗa labarai, ƙungiyoyin farar hula, Majalisar Dokoki ta Ƙasa da sauran cibiyoyin dimokuraɗiyya da su binciki lamarin tare da neman cikakken bayani.
Ya ƙara da cewa rahoton IMF, wanda wakilin asusun a Najeriya, Christian Ebeke, ya gabatar, ya nuna cewa giɓin ya samo asali ne daga wasu manyan ayyukan gwamnati da aka aiwatar ba tare da an haɗa su cikin kasafin kuɗin ƙasa ba.
Har ila yau, Atiku ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na gudanar da manyan kwangiloli da ayyukan raya ƙasa na tiriliyoyin naira ba tare da isasshen sa ido daga hukumomin da ke da alhakin binciken kuɗaɗen gwamnati ba.
Bugu da ƙari, ya zargi gwamnatin tarayya da cire Naira biliyan 800 daga kuɗaɗen da ya kamata a raba wa gwamnatocin jihohi ba tare da amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa ko umarnin kotu ba.
A cewarsa, haɗa wannan Naira biliyan 800 da kuma Naira tiriliyan 8.8 da aka ce ba su shiga kasafin kuɗi ba na nuna alamun ana tara wata babbar taskar kuɗi domin amfani da ita wajen tunkarar zaɓen shekarar 2027.
“Wannan ya saɓa da iƙirarin gwamnatin na aiwatar da gyaran tattalin arziki. Maimakon haka, yana nuna yiwuwar amfani da kuɗaɗen jama’a wajen cimma muradun siyasa,” in ji Atiku.
Sai dai gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan waɗannan zarge-zarge zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
